NLC: Ma’aikata Za Su Bukaci N1m a Matsayin Mafi Karancin Albashi a Kowane Wata

NLC: Ma’aikata Za Su Bukaci N1m a Matsayin Mafi Karancin Albashi a Kowane Wata

  • Joe Ajaero ya nuna ba abin mamaki ba ne su ce dole duk ma’aikaci ya rika karbar akalla N1m a wata
  • Shugaban kungiyar ta NLC ya ce hauhawar farashi da tsadar man fetur ya sa za a bukaci karin kudi sosai
  • Ma’aikata ba su amince ayi masu karin kudin da ba zai saye abinci ko ayi dawainiyar zuwa ofis ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Shugaban kungiyar NLC ta ‘yan kwadago na kasa, Joe Ajaero ya ce abubuwa sun tashi tun bayan hawan Bola Tinubu kan mulki.

A wata hira da Arise tayi da Kwamred Joe Ajaero, shugaban ‘yan kwadagon ya nuna za su bukaci kudi mai yawa a wajen karin albashi.

Kara karanta wannan

Wani jigo a APC ya gargadi Gwamnati, bai so ayi wa ma’aikata karin albashi sosai

Ma'aikata
Ma'aikata na neman karin albashi Hoto: Getty Image
Asali: Getty Images

Za ayi karin albashi ga ma'aikata

Cire tallafin man fetur da tsadar rayuwa su ka jawo ma’aikata suna neman a kara masu albashi, NLC ta ce abubuwa sun yi kunci a yau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Joe Ajaero ya nanata cewa za a duba tsadar rayuwa kafin a yanke mafi karancin albashin da ya kamata gwamnati ta biya ma’aikatanta.

Muddin ba a magance hauhawan farashin da ake fama da ita ba, Ajaero ya ce watakila ‘yan kwadago su bukaci a biya su akalla N1m.

Da aka zanta da shi a gidan talabijn a yammacin Lahadi, Sahara Reporters ta ce Ajaero ya koka game da yadda darajar Naira ta karye.

Maganar shugaban NLC

"Maganar N1m za ta iya tabbata idan darajar Nairar Najeriya ta cigaba da karyewa."

Kara karanta wannan

Kuskuren farko da Tinubu yayi ya jefa mutanen Najeriya a wahala, Hadimin Buhari

"Za ku tuna lokacin mu na tantama a kan N200, 000(a matsayin mafi karancin albashi), a kan N800/N900 ake canza dala."
"Yanzu da muke magana, ana canjin Dala ne a kan N1,400 ko fiye da haka."

-Joe Ajaero

Shinkafa tana tsakanin N60, 000 zuwa N80, 000 a kasuwa, Ajaero ya ce ba za ta yiwu a biya albashin da ba zai saye kayan abinci ba

Fetur ya yi tsada, saboda haka shugaban NLC ya ce dole a biya kudin da zai isa zirga-zirga.

Ma'aikata za su tafi yajin aiki?

Hakan yana zuwa ne bayan an ji labari NLC da TUC sun bada sabon wa’adin komawa yajin-aiki saboda matsanancin kuncin rayuwa.

Gwamnatin Bola Tinubu ta maida martani cewa ba za ta yiwu a biyawa ma’aikata bukunsu duka a lokaci guda ba, dole ayi hakuri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng