Tsadar Rayuwa: Sarkin Musulmi Ya Samo Mafita Ga 'Yan Najeriya

Tsadar Rayuwa: Sarkin Musulmi Ya Samo Mafita Ga 'Yan Najeriya

  • Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi magana kan halin ƙunci da tsadar rayuwa da ƴan Najeriya suka tsinci kansu a ciki a wannan lokacin
  • Alhaji Sa'ad Abubakar III ya bayyana cewa kaucewa Allah da aka yi shi ne babban dalilin da ya sanya aka shiga cikin wannan halin
  • Sarkin Musulmin ya shawarci ƴan Najeriya da su tuba su koma ga Allah domin fita daga cikin wannan halin ƙuncin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad III, ya ce hanya mafi dacewa ta fita daga cikin ƙuncin rayuwa da ƴan Najeriya da dama ke fuskanta ita ce komawa ga Allah wajen yin addu’a.

Ya ce waɗannan wahalhalun sun samo asali ne daga kaucewar da mutane suka yi daga tafarkin Allah, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta shiga sabuwar matsala kan tuhumar tsohon gwamna, bayanai sun fito

Sarkin Musulmi ya shawarci 'yan Najeriya
Sarkin Musulmi ya shawarci 'yan Najeriya su koma ga Allah Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Twitter

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Duk wanda ya bar bautar Allah, to haƙiƙa Allah ba zai kalli ɓangarensa ba, hakan ya tabbata a wurare da dama a cikin Alkur’ani mai girma. Za mu ci gaba da ba gwamnati shawara ta gaskiya."

Sarkin ya bayyana hakan ne a wajen gagarumin taron buɗe masallacin Juma’a da ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa’kamatis Sunnah (JIBWIS) ta gina a Guzape, Abuja.

Wacce mafita Sarkin Musulmi ya kawo?

Sarkin Musulmin wanda ya samu wakilcin tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Alhaji Yayale Ahmed, ya ci gaba da cewa:

“Kowa ya san halin da Najeriya ke ciki a yanzu amma mafita ita ce a koma neman taimakon Allah da addu’a. Duk da haka, bai kamata mu yi domin neman suna ba, amma don addu’a ta gaskiya, saboda Allah ya ce bayan tsanani, sauƙi na tafe.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Arewa, sun sace gomman mutane

Shugaban majalisar malamai ta JIBWIS Sheikh Sani Yahaya Jingir ya shawarci alƙalan Najeriya da su guji cin hanci da rashawa.

Ya kuma umarci sauran jami’an gwamnati da su kasance masu gaskiya da riƙon amana wajen tafiyar da al’amuran ofishinsu.

Sarkin Musulmi Ya Nemi a Duba Jinjirin Watan Sha'aban

A baya an kawo rahoto cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya buƙaci al'ummar musulmi su duba jinjirin watan Sha'aban na shekarar 1445AH.

Sarkin Musulmin ya buƙaci a fara duba jinjirin watan na Sha'aban ne daga ranar Asabar, 10 ga watan Fabrairun 2023, wacce ta yi daidai da 29 ga watan Rajab, 1445AH

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng