Kano: Kujerun Hajji 2,600 Ne Kacal Aka Sayar a Cikin 5,934

Kano: Kujerun Hajji 2,600 Ne Kacal Aka Sayar a Cikin 5,934

  • A yayin da ya rage saura watanni biyu a rufe bayar da bizar zuwa aikin Hajjin 2024, an gano cewa kujeru 2,600 kadai aka siyar a jihar Kano
  • Hukumar alhazai ta kasa ta warewa jihar Kano kujeru 5,934, sai dai daga alama yanayin da kasar ke ciki ya jawo tsaikon siyar da su duka
  • Muhammad Aminu Kabir, a zantawarsa da Legit Hausa ya ce matsin tattalin arziki ya jawo karancin masu zuwa a Hajjin bana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta sayar da kujerun alhazai 2,600 daga cikin kujeru 5,934 da aka warewa jihar domin gudanar da aikin Hajjin 2024.

Darakta janar na hukumar Alhaji Laminu Rabi’u ne ya bayyana hakan a Kano ranar Asabar a wajen kaddamar da shirin horas da maniyyata na shekarar 2024.

Kara karanta wannan

Gasar AFCON: An shiga karancin rigunan Super Eagles a Kano, 'yan kwasuwa sun kwashi ganima

Aikin Hajji 2024 a jihar Kano
An sayar da kujeru 2,6000 cikin 5,934 da aka warewa mahajjatan Kano.
Asali: Twitter

Ana neman mahajjata su halarci horo kan aikin Hajji

Ya kuma tabbatar da cewa hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen aikin Hajjin 2024 a Kano da Saudiyya, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ya kamata mahajjata su kara himma wajen tabbatar da halartar wajen horo akan aikin Hajji da ake yi akai-akai.
“Za a gudanar da horon ne a cibiyoyi 13 da ke jihar Kano; muna kira ga dukkan maniyyatan da su gaggauta zuwa wajen horon don sanin makamar aikin Hajji."

- A cewar Alhaji Rabi’u

Nan da watan Afrilu za a rufe bayar da biza

Ya kuma kara da cewa hukumar ta riga ta kammala dukkan abubuwan da suka dace ta fuskar masauki, ciyarwa da sufuri a lokacin aikin Hajjin 2024.

Rabiu ya bukaci maniyyata da su kasance jakadu nagari na jihar Kano da Najeriya yayin da suke kasar Saudiyya, musamman ta hanyar bin ka’idojin aikin Hajji.

Kara karanta wannan

AFCON: Ana saura kwana 4 aurensa ya rasu, cewar iyalan marigayi Ayuba a Kwara, bayanai sun fito

Ya ce a ranar 29 ga watan Afrilu za a kawo karshen bayar da bizar aikin Hajjin 2024.

Abun da masana ke cewa game da aikin Hajjin bana

Wani mai fashin baki kan tattalin arziki, Muhammad Aminu Kabir, ya ce rashin yawan maniyyata aikin Hajjin bana ba zai rasa nasaba da matsin tattalin da ake ciki ba.

Muhammad Kabir ya yi nuni da cewa, 'yan Najeriya da dama yanzu ta abinci suke yi, ba sa samun damar adana kudi har da zai zarce miliyoyin da za su ne aikin Hajji.

Game da kudin da aka warewa kujerun Hajjin na bana, Kabir ya ce:

"Naira miliyan 4.5 ba kananun kudi ba ne a wannan lokacin, duk da cewa ko za a kai shi sama da hakan za a samu wadanda za su je, amma a yanzu ya yi kudi.
"Matsin tattalin da ake ciki a kasar ya haifar da raguwar maniyyata aikin Hajjin bana, sannan masu daukar nauyin mutane a baya, su ma yanzu ta kansu suke yi."

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnatin Kano ta cika alkawari, ta dira kan rumbun ajiyar masu boye abinci

Muhammad Kabir ya buga misali da yadda darajar Naira ke faduwa a kasuwar duniya, wanda ya ce hakan ne ya sa ba a samu ragin kudin daga naira miliyan 4.5 ba duk da Saudiyya ta yi ragi.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya, da ta yi mai yiwuwa don ganin an daidaita tattalin arzikin kasar wanda ke barazana ga rayuwar 'yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.