An Bayyana Jihohin Arewacin Najeriya 7 da Za Su Sake Shiga Halin Yunwa Nan Gaba, an Fadi Dalili

An Bayyana Jihohin Arewacin Najeriya 7 da Za Su Sake Shiga Halin Yunwa Nan Gaba, an Fadi Dalili

  • Sabon rahoton da Bankin Duniya ya fitar ya nuna halin yunwa da jihohin Arewa guda bakwai za su shiga saboda rashin tsaro
  • Rahoton ya ce akalla jihohi bakwai ne za su kara shiga mawuyacin halin yayin da farashin abinci ke kara hauhawa
  • Jihohin sun hada da Zamfara da Kaduna da Katsina da Adamawa da Borno da Yobe da kuma jihar Sokoto

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Bankin Duniya ya fitar da sabuwar sanarwa kan yunwa da za a sake shiga a jihohin Arewacin Najeriya saboda rashin tsaro.

Bankin ya ce jihohin Katsina da Zamfara da Kaduna na daga cikin wuraren da yunwa zai sake kamari da rashin abinci.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ta yiwu Tinubu ya rufe iyakar Najeriya kan karancin abinci, ya fadi sauran hanyoyi

Jihohin Arewacin Najeriya 7 da za su fuskanci yunwa
Jerin Jihohin Arewa 7 da Za Su Sake Shiga Halin Yunwa. Hoto: Uba Sani, Bola Tinubu, Dauda Lawal.
Asali: Facebook

Wasu jihohin Arewa ke cikin matsala?

Sauran jihohin sun hada da Sokoto da Borno da Adamawa da kuma jihar Yobe da ke Arewa maso Gabashin kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rashin tsaro kama da daga ta’addanci da ‘yan fashin daji da masu garkuwa ya yi tasiri wurin nakasa jihohin, cewar BusinessDay.

Bankin a cikin wani rahoton da ya fitar ya tabbatar da cewa za a sake samun tsadar kayan abinci a wuraren nan gaba.

Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin jihar Katsina ta kafa kwamitin don tabbatar da kayyade farashin kayan masarufi.

Matakin zai kuma dakile hauhawan farashin kaya da kuma siyan kayan abinci mai yawa a cikin jihar, Ask Nigera ta tattaro.

Mene rahoton ke cewa kan jihohin Arewa?

A cewar Bankin Duniya:

“An tabbatar da cewa wasu yankuna a Nahiyar Afirka ta Yamma da kuma Tsakiya za su fuskanci barazanar karancin abinci.

Kara karanta wannan

Hanya 1 tak da gwamnatin tarayya ta dauka don karya farashin kayan abinci, Ministan Yada Labarai

“A Najeriya, jihohin Arewacin kasar kamar Zamfara da Katsina da Sokoto da Adamawa da Yobe da Kaduna da Borno za su fuskanci matsalar tsadar abinci.
“Wannan zai faru ne yayin da yankunan ke fama da rashin tsaro da ya shafi ta’addanci da na ‘yan bindiga.”

Sultan ya bukaci ICPC ta dauki mataki

Kun ji cewa Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar ya bukaci Hukumar ICPC ta dauki mataki kan masu boye kayan abinci.

Sultan ya ce boye kayan abincin da aka fi amfani da su haramun ne kuma dai-dai ya ke da cin hanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.