SERAP Za Ta Kai Karar Gwamnatin Tinubu Gaban Kotu Kan Wani Dalili 1 Tak

SERAP Za Ta Kai Karar Gwamnatin Tinubu Gaban Kotu Kan Wani Dalili 1 Tak

  • Kungiyar SERAP ta ce za ta dauki matakin shari'a a kan gwamnatin Tinubu idan ta kafa dokar amfani da shafukan sada zumunta
  • A baya bayan nan ne Shugaba Tinubu ta bakin Femi Gbajabiamila ya ce kafofin sada zumunta suna haddasa tashin hankula a Najeriya
  • Sai dai SERAP ta ce saka dokar da gwamnatin ke yunkurin yi ya saba wa dokar hakkin bil'adama da ma na kundin tsarin mulkin kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kungiyar kare hakkokin tattalin arziki ta SERAP ta yi barazanar daukar matakin shari'a a kan gwamnatin tarayya kan shirin kafa dokar amfani da shafukan sada zumunta.

An rahoto a baya cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa dole ne a yi dokar amfani da kafafen sada zumunta domin sun zama barazana ga al’umma.

Kara karanta wannan

Gbajabiamila: Shugaban Majalisa Ya Dauki Zafi a Kan Zargin da Ake yi wa Hadimin Tinubu

SERAP za ta dauki matakin doka kan gwamnatin Tinubu
SERAP za ta dauki matakin doka kan gwamnatin Tinubu idan ta kafa dokar amfani da shafukan sada zumunta. Hoto: @SERAPNigeria
Asali: Twitter

Shugaban wanda ya yi magana ta bakin shugaban ma’aikatan fadar sa, Femi Gbajabiamila, ya bayyana haka a wajen kaddamar da wani littafi a jihar Legas a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ya kuma yi Allah wadai da yadda kafafen sada zumunta ke tasiri wajen yada labaran karya, wanda ya haifar da tashin hankali a wasu jihohin.

Martanin SERAP kan kafa dokar amfani da shafukan sada zumunta

Da take mayar da martani, SERAP, ta ce manufar gwamnati ta saba da kundin tsarin mulkin kasar da ka'idojin kare hakkin bil'adama na kasa da kasa.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma'a ta shafinta na X.

Ta ce:

“Barazanar da gwamnatin Tinubu ke yi na kafa dokar amfani da kafafen sada zumunta ya yi hannun riga da kundin tsarin mulkin Najeriya da ka’idojin kare hakkin bil’adama na duniya.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta kirkiri dakarun mutum 7,000 da za su yaki masu tashin farashin Dala

Duba abin da SERAP ta wallafa a kasa:

Bankin CBN ya dakatar da ba gwamnatin Najeriya bashi

A yau Juma'a Legit Hausa ta ruwaito maku cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya ce ba zai kara ba gwamnatin tarayya bashin kudi a tsarin 'Ways and Means' ba.

CBN ya ce yanzu haka yana bin gwamnatin bashin naira tiriliyan 4.36 wanda ba ta biya ba kuma hakan ya sabawa dokar bankin.

'Ways and Means' wani nau'in bashi ne da CBN ke ba gwamnatin tarayya don cika kudin da take bukata wajen aiwatar da kasafin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.