Take hakkokin bil adama: Majalisar dinkin Duniya ta fara binciken kasashe 14, har da Najeriya
Sashin kare hakkokin bil adama na majalisar dinkin Duniya, HRC, zai kaddamar da wani bincike na musamman game da kasashen da suka yi kaurin suna wajen tattake hakkin bil adama, tare da mika rahoton bincikennasu ga majalisar.
Majiyar Legit.com ta ruwaito majalisar ta yi ma wannan aiki na musamman taken; ‘Universal Periodic Review’, manufar aikin shine inganta tsare tsaren kare hakkokin dan adam a kasashen Duniya.
KU KARANTA: Dakarun ‘Civilian JTF’ sun yi ma yan ta’addan Boko Haram kisan gilla a jahar Borno
Majalisar na gudanar da wannan bincike ne a cikin makonni biyu, sau uku a shekara, inda take binciken kasashen goma sha hudu a duk makonni uku, wanda hakan ya bada kasashe Arba’in da biyu a duk shekara.
Daga cikin kasashen da UN za ta bincika akwai Najeriya, Saudi Arabia, Senegal, Mexico, China, Mauritius, Jordan, Malaysia, Central African Republic, Monaco, Belize, Chad, Congo da Malta.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito bayan kowanne shekara hudu da rabi, kasashen dake karkashin majalisar dinkin Duniya su dari da casa’in da uku (193) su kan tattauna a tasakaninsu tare da auna matsayinsu dangane da kare hakkin dan adam.
Majalisar ta bayyana cewa ana shirya wannan tattaunawa ne saboda a baiwa kasashen Duniya dama wajen musayar ilimi ba tare da nuna bambanci ba, bugu da kari a shekarar 2006 aka kafa wannan sashi na binciken hakkokin dan adam.
Haka zalika majalisar ta sanya kasashe 47 a matsayin mambobin dindindin, amma kowace kasa na da ikon shiga a tattauna da ita a duk lokacin da shakara ta zagayo, amma kasashe uku ne ke jagorantar tattaunawar a kowanne zama.
Ana aika kwararrun masu bincike domin su yi ma wakilan kasashen tambayoyi game da wasu abubuwa da suka faru a kasarsa da suka danganci take hakkin bil adama, idan kuma ana tuhumar kasar da laifin ne, sai a bayyana kwararan hujjoji, sai kuma ana baiwa kungiyoyi masu zaman kansu damar halarta.
Daga karshe kuma ana baiwa kasar dake bincike damar yin bayani game da tuhume tuhumen da ake yi mata, bayan nan kuma sai a bata shawarwari da zasu inganta kare hakkin dan adam.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng