Karkashin Buhari, gwamnati ta ci bashin N15.51tn hannun CBN sabanin N33.11tn da ake bin Najeriya

Karkashin Buhari, gwamnati ta ci bashin N15.51tn hannun CBN sabanin N33.11tn da ake bin Najeriya

  • Gwamnati ta ci bashin makudan kudi don gudanar da ayyuka da sauke nauyi
  • Masana sun yi tsokaci kan irin halin da Najeriya ka iya shiga sakamakon wannan bashin
  • Ana bin Najeriya bashin N48tn a cikin gida da waje

Abuja - Jimmillan kudin da gwamnatin tarayya ta karba bashi daga hannun babbar bankin Najeriya CBN ya kai N15.51tn, sabanin N640bn kafin hawa mulkin shugaba Buhari, bayanai daga CBN da Punch ta samu sun nuna.

Wannan bashin na N15.51tn da CBN ke bin gwamnati daban ne da bashin N33.11tn da ake bin Najeriya a bankunan Najeriya da kuma kasashen waje, a cewar ofishin manajin basussuka.

Gwamnati kan karbi bashi hannun bankin CBN domin tafiyar da gwamnati idan aka samu matsala da kasafin kudin shekara.

Sashe na 38 na dokar CBN 2007, bankin na iya baiwa gwamnatin tarayya bashi don amfani idan aka samu matsala da kasafin kudi kuma bankin na iya kara kudn ruwa.

Kara karanta wannan

NNPC zai tashi aiki a Najeriya nan da watanni 6 inji Shugaban NNPC, Mele Kyari

Tsakanin Junairu da Yunin shekarar nan, gwamnatin tarayya ta karbi bashin N2.4tn daga CBN.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Karkashin Buhari, gwamnatin ta ci bashin N15.51tn hannun CBN
Karkashin Buhari, gwamnatin ta ci bashin N15.51tn hannun CBN sabanin N33.11tn da ake bin Najeriya Hoto: CBN

Bayan hawan shugaba Muhammadi Buhari mulki a Yunin 2015, bashin N648.26bn kacal CBN ke bin gwamnati bashi.

Amma zuwa Disamban 2015, bashin ya tashi zuwa N856.33bn, sannan ya sake tashi zuwa N2.23tn a Disamban 2016, bayanin CBN ya nuna.

A 2017 gwamnati ta ci wani sabon bashi N1.08tn, sannan ta kara cin N2.1tn a 2018. A 2019 kuma, gwamnati ta kara karban bashin N3.31tn.

A 2020, gwamnatin Buhari ta sake garzayawa CBN don karban bashin N4.9tn domin magance matsalar rashin kudi.

Tsakanin Junairu da Yunin shekarar nan, gwamnatin tarayya ta karbi bashin N2.4tn daga CBN.

Jimillar bashin da ake bin Najeriya kawo yanzu ya kai N15.51tn.

Gwamnatin tarayya zata ci bashin N4.89trn don daukar nauyin kasafin 2022

Kara karanta wannan

Muna kashe N8m kulli yaumin wajen ciyar da dalibai a jihar Enugu, Minista Sadiya

Gwamnatin tarayya ta bayyana kudirinta na amso rancen cikin gida da na waje na naira tiriliyan 4.89 don samar da kudaden kasafin shekarar 2022 na naira tiriliyan 5.62.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Ministar kudi ta bayyana wannan kudirin a wata takarda da ta mika ga ma’aikatarta ne ga majalisar wakilai ta MTEF da FSP na 2022 zuwa 2024 a ranar Litinin.

Ministar ma’aikatar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, a gabatarwar da tayi ta ce gwamnatin tarayya za ta rage yawan kudaden da take narkawa ma’aikatu, sasanni da hukumomi da naira biliyan 259.31.

Asali: Legit.ng

Online view pixel