Tsadar Rayuwa: Sarkin Musulmi Ya Tura Sako Ga Hukumar ICPC Kan Boye Abinci, Ya Dauki Alkawari
- Yayin da ake fama da tsadar abinci a Najeriya, Sarkin Musulmi ya bukaci daukar mataki kan matsalar boye abinci
- Sultan Sa'ad Abubakar ya bayyana haka ne yayin karbar bakwancin kwamishinan hukumar ICPC a yankin Sokoto
- Ya bukaci Hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ta kaddamar da bincike kan masu boye abincin inda ya ce haramun ne
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Sokoto – Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar ya bukaci daukar mataki kan masu boye kayan abinci a Najeriya.
Sultan ya bukaci Hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ta kaddamar da bincike kan masu boye abincin wanda ya kwatanwa hakan da haramun.
Mene Sultan ke cewa kan tsadar abinci?
Sarkin ya bayyana haka ne yayin karbar bakwancin kwamishinan hukumar da ke kula da Sokoto da Kebbi da Zamfara, Garba Tukur, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa:
“Boye kayayyakin abinci dai-dai ya ke da cin hanci da rashawa, wasu ‘yan kasuwa su na boye kayan don cin riba.
“Na dade ina fatali da wannan hali na wasu da ke boye kayayyakin abinci musamman lokacin watan Ramadan.
“Ko a Musulunce boye kayan abinci da aka fi amfani da su don samun riba haramun ne saboda zai jefa jama’a cikin mawuyacin hali.”
Wane alkawari Sultan ya yi?
Har ila yau, Sultan ya kalubalanci hukumomin ICPC da EFCC da su zage damtse wurin tabbatar da yaki da cin hanci a ko wane mataki.
Ya yi alkawarin cewa sarakunan gargajiya za su hada kai da hukumar ICPC don dakile cin hanci da rashawa a kasar.
Ya kuma gargadi hukumar kan binciken son kai wanda hakan a cewarsa zai kawo nakasu ga nasarar yakar cin hanci, cewar TheCable.
Wannan na zuwa ne yayin da jama’ar Najeriya ke cikin mawuyacin hali tun bayan cire tallafin mai a kasar.
Kano za ta dauki mataki kan boye abinci
Kun ji cewa, hukumar yaki da cin hanci a jihar Kano za ta dauki matakin kwato kayan abinci da aka boye a jihar.
Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado shi ya yi wannan jawabi yayin da mutane ke cikin tsadar rayuwa.
Asali: Legit.ng