Hadadden Saurayi ‘Dan Shekaru 24 Ya Yi Wuff da ‘Yar Shekaru 80, Tana Matukar Son Shi

Hadadden Saurayi ‘Dan Shekaru 24 Ya Yi Wuff da ‘Yar Shekaru 80, Tana Matukar Son Shi

  • Lokacin da Catherine Thomas mai shekaru 80 ta rasa mijinta, ta fada rayuwar kadaici kuma tana bukatar a so ta
  • Mai mashin dinta, George, ya nuna shi 'dan halas ne bayan ta manta makudan kudade a kan babur dinsa
  • Masoyan biyu sun bada labarin yadda suka fada tarkon son junansu da kuma bijirewa hasashen jama'a na samun farin ciki

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani matashi 'dan kasar Tanzaniya yana soyayya da tsohuwar da ta isa yin kaka da shi.

Matashi na soyayya da 'yar shekaru 80
Hadadden Saurayi ‘Dan Shekaru 24 Ya Fada Tarkon Son ‘Yar Shekaru 80, Tana Matukar Son Shi Hoto: Afrimax English
Asali: UGC

Ya aka yi ma'auratan suka fada tarkon soyayya?

George 'dan shekaru 24 da Catherine Thomas, mai shekaru 80, sun kore dukkan shakku ta hanyar nuna cewa soyayya tana cin galaba akan komai, rahoton Afrimax English.

Kara karanta wannan

"Ku Riƙa Faɗin Alheri Kan Kasar Ku" Shugaba Tinubu ya aike da muhimmin saƙo ga 'yan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, soyayyar tasu ta fuskanci kalubale da adawa daga 'yan uwa da al'ummar gari.

A cewar Catherine, wacce ta mallaki 'ya'ya biyar a duniya, a wani bidiyo, ta ce ta shiga rayuwar kadaici bayan mutuwar mijinta.

"Ina bukatan jin cewa ana sona."

George, wanda ya bar makarant ya zama dan achaba, yana daukar Catherine zuwa wajen kasuwancinta a kullun.

Wata rana ana ruwa, Catherine ta manta da jakarta dauke da kudi TSh miliyan 6 (N2,971,485.12) a mashin din George bayan ya kai ta gida.

Ta ce:

"Dare ya yi sosai kuma ana ruwa da zan koma. Na dauki jakar zuwa gidana amma washegari ban gan ta ba."

Catherine ta ce ta manta inda ta bar kudin sannan ta yi tafiyar wata uku a washegari.

Ta ci gaba da cewa:

"Lokacin da na dawo, sai ya dawo da kudin, wanda ta haka ne ya siye zuciyata."

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta kirkiri dakarun mutum 7,000 da za su yaki masu tashin farashin Dala

Daga nan sai Catherine ta tunkari George inda ta nemi ya fara soyayya da ita.

Wani kalubale masoyan suka fuskanta?

'Ya'yan Catherine sun gaza fahimtar dalilin ta na soyayya da wanda suka girma,, kasancewar 'danta na fari shekarunsa 43 yayin da autanta ke da shekaru 35. Saboda haka, suka duba banbancin shekarun.

"'Yar uwar George, Mary, ta ce ta ji babu dadi a lokacin da ta samu labarin soyayyarsu.

Mary ta ce:

"Na fara karbar faruwar abun. Tazarar shekarun na da yawa sosai idan mutum ya girme ka da shekaru 50."

Jama'a na ganin imma dai an yi wa George asiri ne ko kuma yana kwadayin dukiyar Catherine ne.

"A kullun mutane na kokarin lalata abin alkhairi. Da babu shi, da rayuwata ta zama mara amfani," in ji tsohuwar.

Budurwa na neman mijin aure

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata matashiyar budurwa ta bazama neman abokin rayuwa a dandalin X.

Matashiyar mai suna Adeshola Omo-eledumare (@tope_akan a manhajar X), wacce ke cikin shekaru 30 da 'doriya ta bayyana cewa tana bukatar namiji mai alkibla.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng