Hotunan matashi mai shekaru 35 ya yi wuff da tsohuwa mai shekaru 80
- Wani saurayi mai suna Mohammed, dan shekara 35 ya auri wata tsohuwa mai suna Iris, mai shekaru 80 a kasar Egypt
- Sun hadu ne a Facebook, inda suka kulla soyayya mai karfi har ta kai ga ya bar aikinsa don su samu lokacin tarayya da ita
- Sai dai saurayin ya musanta zargin aurenta saboda kudinta, don har musuluntar da tsohuwar yayi kafin ya aureta
Wata tsohuwa mai shekaru 80, ta auri masoyinta mai shekaru 35 da haihuwa a kasar Egypt.
An daura auren Iris Jones da Mohammed Ahmed yanzu haka, bayan sun sha soyayyarsu ta shekara daya da 'yan watanni a kasar Egypt.
Matar mai shekaru 80 da haihuwa, ta hadu da mijin nata wuraren watan Yulin 2019 a wata matattara da ke kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, kuma sun yanke shawarar yin aure a cikin shekarar.
Saurayin ya bar yin aikinsa don ya samu lokacin yin soyayya da masoyiyarsa, ya musanta zargin mutanen da ke cewa saboda kudinta ya aure ta.
Yanzu haka, an riga an daura auren Iris Jone mai shekaru 80 da masoyinta wanda suka hadu a Facebook, Mohammed Ahmed Ibrahim mai shekaru 35.
An daura auren ne bayan Iris ta musulunta, dama bata da wani addini. Bayan sun fara hira da juna a Facebook, ta taho Egypt wurinsa a watan Nuwamban 2019.
Saurayin yana zaune ne a gida mai dakuna 3, tare da iyayensa da kanninsa 3. Bayan ya gabatar da Iris ga mahaifiyarsa, ta nuna amincewarta dari bisa dari matukar hakan zai faranta wa danta rai.
Iris tsohuwar ma'aikaciya ce wacce take zaune a gida mai kimar Ksh miliyan 29, sannan tana samun Ksh 26,000 duk mako. Duk da dai Mohammed ya ce ba saboda kudinta yake sonta ba.
KU KARANTA: Babban mai mukami a Zamfara ya fadi ya mutu a wurin bikin diyar Sanata Yarima (Hotuna)
A wani labari na daban, daya daga cikin manyan 'yan fashin Najeriya, Shina Rambo, ya bayyana a babban birnin Ekiti, yana cewa shifa ya canja, yanzu haka ya koma kira ga addinin Kirista.
Ya yi wannan maganar ranar Lahadi a wani shiri na karshen mako da gidan rediyon Fresh FM, da ke Ado Ekiti, kuma dama shirin babban mawakin yabo ne, sannan mai gidan rediyon da kansa, Yinka Ayefele.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng