Wani matashi dan shekara 16 ya auri tsohuwa ‘yar shekara 71

Wani matashi dan shekara 16 ya auri tsohuwa ‘yar shekara 71

Idan da ranka ka sha kallo, wani labara da hukumar Legit.ng ta yi karo da shi na nunga cewa wani matashi mai shekara 16 a duniya ya auri tsohuwa mai shekara 71 a duniya.

Da fari ýanúwansu basu amince da soyayyar tasu ba a lokacin da suka yi yunkurin auren junansu. Sai dai daga baya sun amince bayan sun yi barazanar kasha kansu idan baá yarje masu da hakan ba.

Inda daga bisani aka daura auren matashin wanda aka ambata da suna Selamat Riayadi da amaryarsa Rohaya.

Sai dai a halin da ake ciki yanzu babu wanda ya san takamammin dalilin da ya sa su ka yi auren ba saboda dukkan ba masu kudi ba ne, duk talakawa ne su.

Wani matashi dan shekara 16 ya auri tsohuwa ‘yar shekara 71
Wani matashi dan shekara 16 ya auri tsohuwa ‘yar shekara 71

'Yan uwan ango Selamat sun biya sadaki 200,000 na kudin kasar Indonesia wadda ake ce ma Indonesian Rupiah (hakan ya zo daidai da kudin fam £11.50 a kudin Ingila).

KU KARANTA KUMA: EFCC tayi yunkuri a kan ‘yan majalisa, tana yunkurin kama wasu Sanatoci

An yi taron biki a gidan shugaban garin mai suna Kuswoyo. Mutane da dama basu yarda da faruwan alámarin ba a lokacin da aka fitar hotuna da bidiyon bikin.

Sai dai an samu tabbaci daga wani wakilin wata kafafen yada labarai na kasan Indonesia wanda ya ce yayi magana da Kuswoyo, kuma ya tabbatar da faruwan haka. Inda shi Kuswoyo ya kara da cewa masoyan sun dauki alkawarin za su kashe kan su ne idan har an ki amince masu su yi aure.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel