Gbajabiamila: Shugaban Majalisa Ya Dauki Zafi a Kan Zargin da Ake yi wa Hadimin Tinubu

Gbajabiamila: Shugaban Majalisa Ya Dauki Zafi a Kan Zargin da Ake yi wa Hadimin Tinubu

  • Wasu sun zargi Femi Gbajabiamila da hannu a badakalar da ake tuhumar Dr. Betta Edu da aikatawa
  • Hadimin shugaban kasar ya gabatar da kan shi domin a bincike shi da nufin ya ba maradansa kunya
  • Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya kare magabacinsa, ya kuma nemi a dauki mataki idan sharri aka yi masa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Wasu sun fito su na jifan Femi Gbajabiamila da rashin gaskiya a matsayinsa na shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa.

Shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya wanke magabacinsa daga zargi, Punch ta fitar da labarin.

Gbajabiamila
Femi Gbajabiamila da Tajudeen Abbas Hoto:@HouseNgr, @femigbaja
Asali: Twitter

Bayan zaman da majalisar wakilai tayi, Hon. Tajudeen Abbas ya bukaci jami’an tsaro su binciki zargin da ake yi wa Femi Gbajabiamila.

Kara karanta wannan

Gwamnoni ga Tinubu: Ga hanyar shawo kan matsalar tsadar abinci da tattalin arziki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana a ranar Alhamis wajen taron manema labarai, Abbas ya ce zargin nan za su iya taba kimar damukaradiyyar kasar.

Shugaban majalisar ya ce ana maraba da caccakar da aka yi na mutunci domin ayi gyara, amma ya yi tir game da yada labaran bogi.

Na hudu a kasar yana ganin ana kokarin a bata sunan Gbajabiamila ne wanda ya rike shugabancin majalisa kafin zuwansa a 2023.

Femi Gbajabiamila v Betta Edu

Wasu sun fito suna zargin cewa hadimin shugaban kasar yana da hannu a badakalar da ake zargin Betta Edu ta tafka a kujerar minista.

Wadannan tuhume-tuhume su ka jawo Dr. Edu ta rasa kujerarta, bayan nan sai aka fara huro wuta a binciki tsohon shugaban majalisar.

Shugaban majalisa ya kare Gbajabiamila

Wadanda suka yi aiki da shi na fiye da shekaru gome sun shaida kishin kasa da darajarsa.

Kara karanta wannan

An shiga rudani kan batun mutuwar babban basarake a Najeriya, an fadi gaskiyar abin da ya same shi

Amincewa da ya yi bisa zabin kansa domin jami’an tsaro su bincike shi ya nuna gaskiya da mutuncinsa.

Ina kira ga jami’an tsaro su yi aiki da kyau da gaggawa domin binciken duk abubuwan da ya fada.

Solacebase ta ce shugaban majalisar ya ce idan har zargin ba su tabbata ba, jami’an tsaro su cafko masu hannu da jifar cin mutuncin.

Hon. Gbajabiamila ya fitar da wasika ya na nuna cewa a shirye yake da a bincike shi.

Taron Gwamnonin Najeriya

Ana da labari gwamnonin jihohi sun yi kira ga shugaban kasa kuma za su kawo dabaru da tsare-tsaren da za su tilasta arahar abinci.

Mai girma gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya jagoranci zaman da aka yi a makon nan a matsayin shugaban kungiyar NGF.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng