Mahara Sun Sake Hallaka Fitaccen Basarake a Jihar Arewa, Bayanai Sun Fito
- Wasu 'yan bindiga sun sake hallaka wani fitaccen basarake a jihar Kogi a yau Laraba 7 ga watan Faburairu
- Maharan sun farmaki Elepe na Ohi-Ogidi, Cif Olayinka Ojo a karamar hukumar Ijumu da ke jihar
- Kwamishinan yada labarai, Kingsley Fanwo shi ya bayyana haka a yau Laraba 7 ga watan Faburairu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kogi - An shiga cikin wani irin yanayi bayan 'yan bindiga sun hallaka wani mai sarautar gargajiya a jihar Kogi.
Maharan sun farmaki Elepe na Ohi-Ogidi, Cif Olayinka Ojo a karamar hukumar Ijumu da ke jihar, cewar Punch.
Yaushe maharan suka kai harin a Kogi?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar, Kingsley Fanwo ya fitar a yau Laraba 7 ga watan Faburairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan ya yi Allah wadai da harin inda ya bukaci jami'an tsaro da su kara kaimi wurin zakulo su tare da hukunta su, cewar Tribune.
Fanwo ya ce gwamnatin jihar ya yi Allah wadai da harin inda ya ce ana kai harin ne don kawo cikas a kokarin gwamnatin na kare lafiyar jama'a.
Martanin gwamnatin jihar Kogi kan harin
Ya ce:
"Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Usman Ododo ya umarci jami'an tsaro da su yi gaggawar zakulo wadanda suka aikata laifin don fuskantar hukunci.
"Duk da cewa hakan ba zai dawo da wanda ya mutu ba, hakan zai kara aminci ga mutanen jihar kan jami'an tsaro."
Ya bukaci al'ummar Ogidi da karamar hukumar Ijumu da su kwantar da hankulansu ba tare da daukar doka a hannu ba, News Now ta tattaro.
Mahara sun hallaka sarakuna 2 a Ekiti
Kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun yi ajalin wasu manyan sarakunan gargajiya biyu a jihar Ekiti.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin 29 ga watan Janairu yayin da sarakan ke dawo da daga taron dakile matsalar tsaro.
Maharan sun farmaki sarakan ne guda uku yayin da daya daga cikinsu ya sha da kyar inda suka halllaka biyu daga ciki.
Asali: Legit.ng