Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Wani Kauyen Nasarawa, Sun Kashe Sojoji da Ƴan Banga
- Wasu 'yan bindiga sun kai hari kauyen Umaisha da ke karamar hukumar Toto, jihar Nasarawa kuma sun kashe sojoji da 'yan banga
- Rahotanni sun bayyana cewa sojojin da 'yan bangar sun fita rangadi a cikin garin lokacin da 'yan bindigar suka yi masu kwanton bauna
- Ƙauyuka a karamar hukumar Toto musamman Okudu da Katakpa na fuskantar hare-haren 'yan bindiga da kuma rikicin kabilanci
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Nasarawa - Mutane sun shiga tashin hankali a jihar Nasarawa bayan da wasu 'yan bindiga suka kashe jami'an soji uku da 'yan banga biyu.
Lamarin ya faru ne a gundumar Umaisha, karamar hukumar Toto da ke jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Rahotanni sun bayyana cewa a ranar 1 ga watan Fabrairu, wasu 'yan bindiga sun halaka mutane uku tare da lalata kayayyaki na miliyoyin naira a kauyen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hare-haren da aka kai kauyukan Toto
An kuma gano cewa 'yan bindigar sun kuma kai wani farmaki kauyen Okudu inda suka kashe mutane da dama.
An jibge wasu jami'an sojoji a ƙauyukan Katakpa da Okudu domin dawo da zaman lafiya biyo bayan rikicin yanki da ya barke tsakanin garuruwan biyu.
Shugaban karamar hukumar Toto, Mr. Abdullahi Aliyu-Tashas, wanda ya tabbatar da kisan sojojin, ya shaidawa Daily Trust cewa 'yan bindigar sun yi wa sojojin kwanton bauna.
Ya ce:
"Yanzu haka da nake maka magana, ina tare da motar asibiti da ke dauke da gawarwakin sojijin, kuma gwamnatin jihar ta shiga cikin lamarin."
Kungiyar BCDU ta aika sako ga Gwamna Sule
Ya kuma ce jami'an tsaro sun cika ko ina a kauyen Katakpa domin dakile tashin wata tarzomar biyo bayan kashe sojojin.
A hannu daya, kungiyar raya al'adu ta Bassa (BCDU) ta nemi Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nassarawa da ya gaggauta kama wadanda suka kai farmaki kauyen Katakpa.
Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwar dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Mr. Emmanuel M Gbaji wacce aka rabawa manema labarai a ranar Laraba.
Katsina: Yan bindiga sun saki bidiyon 'yan mata 63 da suka sace
A wani labarin kuma, 'yan bindigar da suka sace amarya da 'yan matan daukar amarya 63 a Katsina sun saki wani bidiyo tare da gargadar gwamnatin jihar.
Kamar yadda aka gani a cikin bidiyon, 'yan matan na cikin tashin hankali, kuma 'yan bindigar sun yi barazanar sake aurar da amaryar idan ba a biya kudin fansa ba.
Asali: Legit.ng