Kwanton bauna: Soji sun yi wa mayakan ISWAP raga-raga a hanyarsu ta kai farmaki Ngamdu

Kwanton bauna: Soji sun yi wa mayakan ISWAP raga-raga a hanyarsu ta kai farmaki Ngamdu

  • Jiragen sojojin NAF masu saukar angulu tare da taimakon sojin kasa, sun ragargaji 'yan ta'addan ISWAP
  • Sojojin sun yi wa 'yan ta'addan kwanton bauna ne bayan sun samu labarin za su kai farmaki garin Ngamdu
  • Cike da tarin nasara dakarun suka ragargaji 'yan ta'addan da ke motocin yaki kuma da yawansu suka rasa rayukansu

Ngamdu, Borno - Jiragen yaki biyu masu saukar angulu na rundunar sojin saman Najeriya, NAF, a ranar Talata sun bankado mummunan farmakin da 'yan ta'adda suka kai garin Ngamdu, garin da ke da iyaka da jihohin Yobe da Borno.

PRNigeria ta tattaro cewa 'yan ta'addan sun yi kokarin kai farmaki sansanin sojoji da ke yankin kafin dakarun sojin su bankado mugun nufin.

Sojoji sun yi wa mayakan ISWAP kwanton bauna kan hanyarsu ta kai farmaki Ngamdu
Sojoji sun yi wa mayakan ISWAP kwanton bauna kan hanyarsu ta kai farmaki Ngamdu. Hoto daga PRNigeria.com
Asali: UGC

An gano cewa mayakan ta'addancin Islamic State of West Africa Province (ISWAP) ne suka shirya farmakin kuma jiragen sojojin tare da taimakon sojin kasa da ke sansanin Ngamdu suka dakile.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun fafata da Boko Haram, an ragargaji 'yan Boko Haram da yawa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiyar tsaro ta sanar da PRNigeria cewa 'yan ta'addan ISWAP sun tsinkayi garin a MRAP da kuma motocin yaki.

"Da gaske mun yi musu kwanton bauna lokacin da bayanan sirri suka tabbatar mana da hanyar da za su bi. Sun shiga garin Ngamdu ta hanyar Goniri zuwa Damboa a motoci masu yawa da suka hada da MRAP da motocin yaki.
“A yayin da suka karato, dakarun mu sun fara aiki, daga sama da kuma kasa inda suka dinga sakarwa 'yan ta'adda wuta.
“A halin yanzu muna kwashe gawawwakinsu yayin da tuni hankula suka kwanta a garin," majiyar tace.

Mata 6 da kananan yara 9 sun tsero daga hannun Boko Haram

A wani labari na daban, mata shida tare da yara kanana 9 da aka sace a yankin arewa maso gabas sun tsero daga hannun miyagun da suka sace su. Sun kwashe kwanaki shida suna tafiya a daji kafin su samu 'yanci a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

An sheke kwamandojin ISWAP 3, Yaya Ebraheem, Baba Chattimari, Abu Oubaida da wasu 21

Mutum 15 din an sace su daban-daban ne a gonakinsu da ke kauyukan Takulashi a Chibok , jihar Borno da kuma Cofure da ke karamar hukumar Hong ta jihar Adamawa watanni da yawa da suka gabata, Channels TV ta wallafa.

Uku daga cikin wadanda aka sacen an kwashe su ne tare da kananan 'ya'yansu biyar yayin wani samame da 'yan ta'addan suka kai Takulashi a watan Oktoban shekarar da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel