Gwamna Ya Zage Yayi Karin Albashi, Ma’aikatan Jihar Sun Raina N10, 000 a Wata 3
- Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da cewa za a biya ma’aikata N10, 000 a rage radadin tsadar fetur
- Shugabannin ‘yan kwadago sun ki amincewa da karin da sunan cewa ba a kammala tattaunawa ba
- A wurin gwamnatin Jigawa, babu wata tattaunawa da ta rage tsakaninta da ma’aikatan da ke jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Jigawa - Kungiyar kwadago ta reshen jihar Jigawa, ba ta amince da karin N10, 000 da gwamnatin Malam Umar Namadi tayi ba.
Kungiyar NLC ta fitar da jawabi na musamman a ranar Talata, tayi watsi da karin da aka yi, rahoton ya fito a jaridar Tribune.
NLC da TUC sun yi zama a Jigawa
‘Yan kwadagon sun cin ma matsaya ne bayan wani zama da aka yi da sauran shugabannin kungiyar TUC ta ‘yan kasuwa jiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin jihar Jigawa tayi wannan kari ne sakamakon tallafin man fetur da gwamnatin Bola Tinubu ta cire a Mayun 2023.
Shugabanni da sakatarorin NLC da TUC sun sa hannu a wannan matsaya da aka cin ma na kin karbar karin albashin da aka yi.
Korafin ma'aikata a kan karin albashi
Kungiyoyin ma’aikatan sun ce ba a kammala magana ba kurum sai suka ji gwamnati ta fitar da sanarwa, zancen da aka karyata.
Jawabin ya ce kwamitin da aka kafa a kan batun karin albashin ya dauki tsawon lokaci domin ganin an yi nasara a Jigawa.
Sai dai Daily Trust tace har yau gwamnatin Namadi ba ta ba kungiyoyin NLC da TUC amsar takardun da suka aika masu a baya ba.
Jawabin shugabannin NLC
"Abin mamaki, yayin da ake cikin tattaunawa, sai mu ka ji Kwamishinan labarai, matasa da al’adu, Hon. Sagiru Musa, ya bada sanarwar karin N10, 000 na tsawon watanni uku a matsayin karin kudi."
“Yana da muhimmanci al’umma su sani cewa kungiyoyin kwadago ba su sa hannu a wata yarjejeniya da gwamnatin jihar Jigawa a kan karin na N10, 000;”
“Kwamitin tattaunawar bai kammala aikinsa ba”
- NLC
Mutane sun koma zanga-zanga
Ana da labarin kafa kwamitin da zai magance matsalar tsada da rashin abinci da aka ji zanga-zanga a garuruwan Minna da Kano.
Irinsu Yemi Cardoso, Wale Edun, Nuhu Ribadu, Abubakar Kyari, Aliyu Sabi da Mariya Mahmoud da Atiku Bagudu su na kwamitin.
Asali: Legit.ng