Tura Ta Kai Bango: Hafsoshin Tsaro Za Su Bayyana Gaban Majalisar Dattawa Kan Abu 1 Tak
- Majalisar dattawa ta shirya zama da manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan kan halin rashin tsaron da ake ciki a ƙasar nan
- Manyan hafsoshin tsaron dai za su bayyana a gaban ƴan majalisar ne domin yin bayani kan matsalar rashin tsaron da ta addabi ƙasar nan
- Bayyanar manyan hafsoshin dai na zuwa ne bayan a makon da ya gabata ƴan majalisar sun amince da ƙudurin neman su bayyana a gaban majalisar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta bayyana cewa za ta titsiye hafsoshin tsaron ƙasar nan a ranakun Laraba da Alhamis kan halin da ake ciki na rashin tsaro a ƙasar nan.
Sanata Tokunbo Abiru ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da yake sanar da ɗage zaman tattaunawa tsakanin kwamitin majalisar dattawa kan harkokin banki, inshora, da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗi daga ranar Talata zuwa Juma’a ta wannan mako, cewar rahoton The Punch.
Abiru, wanda shi ne shugaban kwamitin, ya shaida wa manema labarai cewa, an ɗage zaman tattaunawa da gwamnan babban bankin na CBN, Olayemi Cardoso zuwa Juma’a, tun da an shirya ganawa da hafsoshin tsaron a ranakun Laraba da Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa hafsoshin tsaron za su bayyana gaban majalisar?
Majalisar dattijawa a makon da ya gabata ta amince da ƙudurin gayyatar hafsoshin tsaron da su bayyana a gabanta domin yin bayani a kan tabarbarewar tsaro a ƙasar nan, rahoton Thisday ya tabbatar.
Abiru ya bayyana cewa:
"Da mun sanya Laraba ko Alhamis a wannan makon a matsayin sabuwar rana don tattaunawa amma majalisar dattawa ta ware kwanaki biyu don tattaunawa mai ma'ana tare da hafsoshin tsaro."
"Wannan ya sa a ƙarshe muka yanke ranar Juma’a ta wannan makon domin mu tattauna da gwamnan CBN da ƙarfe 9:00 na safe."
An Gabatar da Ƙudirin Mallakar Bindiga a Majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Ned Nwoko ya gabatar da ƙudirin ba ƴan Najeriya damar mallakar bindiga.
Sanatan mai wakiltar mazaɓar Delta ta Arewa ya gabatar da ƙudurin ne duba da yadda matsalar tsaro ta taɓarɓare a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng