Gwamnan Kano Zai Je Ya Samu Tinubu Su Yi Kus-Kus Kan Wata Gagarumar Matsala 1 Tak

Gwamnan Kano Zai Je Ya Samu Tinubu Su Yi Kus-Kus Kan Wata Gagarumar Matsala 1 Tak

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya magantu kan halin da 'yan Najeriya ke ciki na tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki
  • Abba Yusuf ya bayyana cewa zai je ya samu Shugaban kasa Bola Tinubu domin sanar da shi halin da al'ummar Kano ke ciki na wahala
  • Sai dai kuma, ya sha alwashin yin duk mai yiwuwa domin ganin ya samawa al'ummar jiharsa maslaha na kangin da suke ciki

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, ya ce zai gana da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan matsin tattalin arziki da wahalar da 'yan Najeriya ke sha.

Abba Gida-Gida ya ce zai yi tattaki har zuwa Abuja domin sanar da Tinubu irin wahalar da mutanen jihar Kano ke sha saboda tsadar rayuwa da nufin sama masu mafita.

Kara karanta wannan

Ramadan: Abba ya zauna da ‘yan kasuwan Kano, ya roki a fito da abinci da aka boye

Gwamnan Kano zai hadu da Tinubu
Gwamnan Kano Zai Je Ya Samu Tinubu Kan Wani Muhimmin Abu 1 Tak Hoto: Abba Kabir Yusuf Hoto: @Dolusegun16/@Kyusufabba
Asali: Twitter

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da 'yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a gidan gwamnatin jihar a ranar Litinin, 5 ga watan Fabrairu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Yusuf ya ce:

“Zan gana da shugaban kasa Tinubu da kaina domin yi masa bayani game da wahalhalun da al’ummar jihar Kano ke fuskanta na hauhawar farashin kayayyaki da nufin samar damafita ga jama’a."

Me Abba ya ce kan tsadar rayuwa?

Ya koka da yadda farashin kayan abinci da abubuwan bukata na yau da kullun ke karuwa.

Saboda haka, ya ce akwai bukatar a hada kai cikin gaggawa domin samar da mafita mai 'dorewa ga matsalolin tattalin arziki.

Gwamnan ya ci gaba da cewa:

"Manufar wannan taro ita ce a saita tsarin yadda za a magance matsalar hauhawar farashin kayayyaki saboda mutane na shan wahala matuka kuma muna bukatar yin wani abu kan wannan."

Kara karanta wannan

Neman tabarraki: Shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya, Ali Nuhu ya ziyarci Sarkin Kano

Gwamnan Kano ya yi kira ga 'yan kasuwa

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta yi duk mai yiwuwa don samar da yanayi mai kyau ga ‘yan kasuwa, rahoton Independent.

Sai dai kuma, gwamnan ya bukaci 'yan kasuwa da su bayar da hadin kai ta hanyar biyan kudin haraji yadda ya kamata, don gwamnatin ta samu kudaden shida za ta gudanar da aiki yadda ya kamata.

Gwamnan ya bayyana aniyarsa na ganin jihar ta kasance kan matsayin cibiyar kasuwanci.

Gwamnan Sokoto zai yi ciyarwar Ramadan

A wnai labarin kuma, gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi, ya yi alkawarin ɗaukar masallaci daya a kowace karamar hukumar jihar domin ciyar da abinci kyauta a cikin watan Ramadan.

Ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da ya karbi bakuncin mutanen kananan hukumomin Arewa da Dandi, wadanda suka kai masa ziyarar godiya yau Litinin, Vanguard ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng