Kotu Ta Yanke Hukuncin Daurin Rai da Rai Ga Matar Aure Kan Mutuwar ‘Dan Kishiyarta a Kano
- Mai shari’a Halima Sulaiman ta babbar kotun Kano ta yankewa wata matar aure hukuncin daurin rai da rai
- Ana zargin Rukayya Abubakar da kashe 'dan kishiyarta ta hanyar jefa shi a cikin wata rijiya a shekarar 2021
- Haka kuma, an gurfanar da wata matar aure kan zargin hallaka dan kishiyarta ta hanyar saka masa guba
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Kano - Wata babbar kotun Kano karkashin jagorancin Mai shari’a Halima Sulaiman ta hukunta wata matar aure, Rukayya Abubakar, kan kisan ‘dan kishiyarta.
Kotun ta umurci mai laifin da ta kare sauran rayuwarta a gidan yari, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Lauya mai shigar da kara, Barista Rabia Sa’ad, ta shaida wa kotun cewa a shekarar 2021, Rukayya ta jefa ‘dan kishiyarta cikin rijiya, lamarin da ya kai ga mutuwarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Sa’ad, laifin da wacce ake tuhumar ta aikata ya sabawa sashe na 221 na kundin laifuffuka.
A yayin shari’ar, lauyan mai gabatar da kara ya gabatar da shaidu hudu a gaban kotun.
Lauyan da ke kare wacce ake kara, Barista Rilwan Muhammad, ya roki kotun da ta yi sassauci domin wacce aka yankewa hukuncin uwa ce mai ‘ya’ya da dama da za ta kula da su.
An sake gurfanar da matar aure a kotu
Har ila yau, an gurfanar da wata matar aure a gaban kuliya bisa laifin kashe dan kishiyarta.
Sai dai lauyan masu shigar da kara, Barista Lamido Soron Dinki, ya sanar da kotun cewa wacce ake karar ta saka wa ‘dan kishiyarta, jariri mai suna Naziru Ashiru guba har ya yi dalilin mutuwarsa.
A cewar Soron-Dinki, laifin ya yi karo da sashe na 221 na kundin laifuffuka.
Wacce ake karar ta karyata aikata laifin da ake tuhumarta a kansa.
Lauyan wacce ake kara Barista Samir Rabiu ya nemi a ba ta beli inda kotun ta amsa.
Alkalin kotun, Mai shari’a Zuwaira Yusuf ta bayar da umarnin cewa a tsare wacce ake kara a gidan gyara hali. Ta kuma dage sauraron karar zuwa ranar 5 ga Maris, 2024.
An yankewa matar aure hukunci mai tsauri
A wani labarin, an yankewa wata malamar addinin Musulunci a Uyghur da ke kasar China hukunci kan zargin tsorata kasa.
An yankewa Rahila Davut mai shekaru 57 wacce ke koyarwa a jami’ar Xinjianghukuncin daurin rai da rai.
Asali: Legit.ng