Kogi: Yan Bindiga Sun Sace Fasinjojin Wasu Manyan Motoci Guda Biyu a Hanyar Zuwa Abuja
- Yan bindiga sun tare wasu manyan motoci na kamfanin GIG da ABC Transport a Kogi inda suka yi awon gaba da fasinjoji gaba daya
- Motocin sun dauko fasinjoji ne daga jihar Umuahia za su je Abuja lokacin da abin ya faru, kamar yadda rundunar 'yan sanda ta tabbatar
- Wani mutum da abin ya rutsa da matarsa ya sanar da cewa 'yan bindigar sun kirasa a waya tare da neman naira miliyan 15 kudin fansa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kogi - An yi garkuwa da wasu matafiya daga Umuahia na jihar Abia a cikin wasu manyan motocin alfarma guda biyu a Inyele Eteke da ke karamar hukumar Olalamaboro ta jihar Kogi.
Wakilin jaridar The Punch ya tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a 3 ga Fabrairu, 2024.
Wani mai ma'abocin shafukan sada zumunta, Chude Nnamdi, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na X, ya ce motocin bas guda biyu na kamfanin GIG da ABC Transport ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Chude ya ce akwai matar wani mabiyinsa a cikin fasinjojin da aka sace amma bai iya tantance adadin mutanen da ke cikin motocin biyu ba.
Rundunar 'yan sanda ta magantu kan harin
Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, yayin da ta tabbatar da faruwar lamarin, ita ma ba ta iya tantance adadin mutanen da ke cikin motocin ba.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP William Aya, ya ce 'yan sanda sun ga motocin bas guda biyu amma babu mutane a cikin.
Masu garkuwan sun nemi naira miliyan 15
Chude Nnamdi ya yi karin bayani da cewa:
"Rahoton da ke iso gareni a safiyar yau na nuni da cewa wasu masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wata motar bas din GIG da ABC dake kan hanyar zuwa Abuja jiya a jihar Kogi.
Wanda ya aika masa da sakon ya rubuta cewa:
“An yi garkuwa da mutanen da ke cikin bas din GIG da ta bar Umuahia da karfe 7:30 na safe a jihar Kogi. Kamfanin ya ce yana bin diddigin motar."
"Masu garkuwa da mutanen sun kirani a waya da safiyar yau ta wayar matata kuma suna neman naira miliyan 15 kudin fansa.”
Ga abinda Chude ya wallafa:
Saurayi ya datse kan budurwarsa a jihar Bayelsa
A wani labarin kuma, rundunar 'yan sanda ta ce ta kama wani matashi mai suna Jony wanda ake zargi da datse kan budurwarsa a karamar hukumar Sagbama ta jihar Bayelsa.
An ruwaito cewa Jony ya kashe budurwar ne da tsakar dare inda ya yi yunkurin tserewa washe gari, amma 'yan unguwar suka tare shi har sai da 'yan sanda suka je wajen.
Asali: Legit.ng