Bashin da Ake Bin Gwamnatin Tarayya da Jihohi Ya Kusa Haura Naira Tiriliyan 107, an Gano Dalili

Bashin da Ake Bin Gwamnatin Tarayya da Jihohi Ya Kusa Haura Naira Tiriliyan 107, an Gano Dalili

  • Da alama bashin da ake bin gwamnatin tarayya da jihohi zai iya haura naira tiriliyan 107 nan ba da jumawa ba, kamar yadda bincike ya nuna
  • A halin yanzu dai ana bin tarayya da jihohi bashin naira tiriliyan 87.91, yayin da a watan Disamba 2023 Tinubu ya karbi bashin dala biliyan 7.8
  • An ruwaito cewa darajar bashin na hauhuwa ne dai dai da darajar Naira akan Dala a kasuwar canji, wanda a baya aka ga karyewar kudin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jimillar basussukan da ake bin gwamnatin tarayya da na jihohi na iya haura naira tiriliyan 107.38 nan ba da jimawa ba bayan amincewa da sabon rance ga gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Kogi: Yan bindiga sun sace fasinjojin wasu manyan motoci guda biyu a hanyar zuwa Abuja

Wannan na zuwa bayan da majalisar dattawa a Disamba 2023, ta amince da bukatar Shugaba Tinubu na neman rancen dala biliyan 7.8 da kuma euro miliyan 100.

Bashin da ake bin Najeriya ya kusa naira tiriliyan 107
Da zaran dala ta tashi, darajar bashin da ake bin Najeriya shima yana karuwa. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Bashin na a matsayin wani bangare na shirin karbo bashin gwamnatin tarayya na 2022-2024, da nufin samar da gine gine, bunkasa kiwon lafiya, ilimi, noma, yaki da rashin tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yawan bashin da ake bin Najeriya daga 2022 zuwa 2023

Adadin bashin da ake bin Najeriya a karshen watan Satumbar 2023 ya kai naira tiriliyan 87.91, kamar yadda bayanai daga ofishin kula da basussuka suka nuna.

Bayani kan wannan bashin ya nuna jimillar bashin daga aka karbo daga waje naira tiriliyan 31.98 ($41.59bn) da kuma bashin cikin gida naira tiriliyan 55.93.

Tsakanin Janairu 2022 zuwa Satumba 2023, gwamnatin tarayya ta kara dala biliyan 3.20 akan bashin da ta karba daga waje daga dala biliyan 38.39 zuwa dala biliyan 41.59.

Kara karanta wannan

Babban bankin Najeriya CBN ya gano wani dalili 1 tak da ke jawo faduwar darajar Naira

Darajar bashin na hauhawa idan darajar Naira ta fadi

Kara yawan basussuka zuwa naira tiriliyan 107.38 zai kai kashi 53.06% na GDPn kasar na shekarar 2022 na naira tiriliyan 202.37.

Punch ta tattara rahoton ba tare da yin amfani da farashin dala na ranar Juma’a, 2, 2024 lokacin da Naira ta rufe a kan N1435.53/$, The Cable ta ruwaito farashin.

Hakan ya biyo bayan kyakkyawan fatan da ake yi na babban bankin CBN ya daidaita farashin canjin dalar a kasuwar hada-hadar kudi.

An gano badakalar naira biliyan 12 a Kotun Kolin Najeriya

A wani labarin kuma, ofishin babban mai bincike na kasa (OAuGF) ya gano yadda wasu shugabannin Kotun Koli suka batar da sama da naira biliyan 12 ta hanyar da bata dace ba.

Ba wannan kadai ba, ofishin ya kuma bankado yadda aka cefanar da wasu kadarori na kotun a Legas da yadda mutanen suka rinka amfani da kayan gwamnati ba bisa ka'ida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.