Kiwon Lafiya: Nau'ikan abinci 3 da su ke rage nauyin jiki

Kiwon Lafiya: Nau'ikan abinci 3 da su ke rage nauyin jiki

Akwai nau'ikan abinci da su ke kunshe da sinadaran gina jiki kuma wanda su ke taimakawa wajen kara karfin kashi, kariya daga cututtuka, karfin gani na ido kuma su bayar da kwanciyar hankali da nutsuwa ga mai amfani da su.

Ga jerin nau'ikan abinci kala uku wadanda su ke taimakawa wajen rage nauyi jiki saboda da yawan mutane su na kukan jikin su ya mu su nauyi ta yadda ba kowane irin motsi su ke iyawa ba.

1.Alkama

Kiwon Lafiya: Nau'ikan abinci 3 da su ke rage nauyin jiki
Kiwon Lafiya: Nau'ikan abinci 3 da su ke rage nauyin jiki

Alkama ta na kunshe da sinadarai wadanda su ke taimakawa mai amfani da su tsawon yini da su ke bunkasa ingancin kayan cikin sa da karfafa su wajen kone daskarerren maiko.

2.Kayan itatuwa (Kayan marmari)

Kiwon Lafiya: Nau'ikan abinci 3 da su ke rage nauyin jiki
Kiwon Lafiya: Nau'ikan abinci 3 da su ke rage nauyin jiki

Babu wata matsala don mutum ya sha maiko don idan har za ka sha maiko kuma ya sha dan itacen kayan maramari to ba shi da wata matsalar jin nauyin jiki. Su kayan itatuwa irin su inibi, abarba, gwanda, kankana, lemon bawo da na tsami su na dauke ne da da sinadarin Oleic acid wanda ya ke kone duk wani maiko da ke cikin mutum sannan kuma ya bunkasa lafiyar jinin jikin mutum.

3.Kifi

Kiwon Lafiya: Nau'ikan abinci 3 da su ke rage nauyin jiki
Kiwon Lafiya: Nau'ikan abinci 3 da su ke rage nauyin jiki

Yin amfani da tsokar kifi ita kadai ba ta rage nauyin jiki, sai dai ta na da sinadarai na PROTEIN wanda su ke taimakawa wajen kara lafiyar jiki, inganta yalwar jini a jiki da taimakawa wajen mayar da tsokar rauni da mutum ya samu.

KU KARANTA: Mutum 4 sun rasa rayukan su sanadiyar fashewar tukunyar gas

Ita tsokar kifi tana da sinadarai na gina jikin dan Adam kuma duk yawan amfani da mutum zai yi da ita ba za ta kara masa nauyin jiki ba saboda babu maiko wanda daman maiko shine abu mai assasa jikin mutum ya yi nauyi.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng