Tashin Hankali Yayin da Saurayi Ya Gutsire Kan Budurwarsa a Bayelsa
- Rahotanni sun bayyana cewa wani mutum da aka bayyana sunansa da Tony ya datse kan budurwarsa a garin Sagbama da ke jihar Bayelsa
- Ana zargin Tony ya kashe Maxuel Ebibraladei da misalin karfe 3 na safiyar ranar Asabar a cewar makwabtan masoyansa
- Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da cewa rundunar za ta fitar da sanarwa kan binciken lamarin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Bayelsa - A karshen makon da ya gabata ne wani mutum da aka bayyana sunansa da Tony ya fille kan budurwarsa a unguwar Kabeama da ke karamar hukumar Sagbama ta jihar Bayelsa.
Ko da yake har yanzu ba a samu cikakken bayanai game da wannan mumunar lamarin ba, amma Aminiya ta tattaro cewa marigayiyar, Maxuel Ebibraladei ta haihu da Tony.
Mazauna garin sun kama Tony kafin ya tsere
Ana zargin masoyinta ne ya kashe ta da misalin karfe 3 na safiyar ranar Asabar a cewar makwabta da suka tsinkayi lamarin da gari ya waye.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun bayyana cewa mazauna garin sun kama Tony kafin ya tsere kuma suka mika shi ga ‘yan sanda.
Vanguard ta ruwaito cewa an ajiye gawar marigayiyar a dakin ajiye gawa na cibiyar lafiya ta tarayya da ke Yenagoa.
Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin
A hannu daya kuma shi Tony, wanda ake zargin na tsare a sashin binciken manyan laifuka na jihar (CID).
Wani mazaunin garin ya shaidawa Daily Trust cewa:
“Ba mu san abin da ya faru tsakanin masoyan biyu da zai sa ya yanke kan mahaifiyar yaronsa ba domin su biyun suna da shiru-shiru da saukin kai."
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa, ASP Musa Muhammed, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce rundunar za ta fitar da sanarwa kan lamarin.
Boko Haram sun kashe mutum biyu a Yobe
A wai labarin kuma, mayakan Boko Haram sun kai hari wata cibiyar tattara sakamakon zabe da ke Kuareta wanda ke nesa da garin Damaturu, jihar Yobe.
An ruwaito cewa mayakan sun kai farmakin ana tsaka da tattara sakamakon zabe, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum biyu.
Asali: Legit.ng