Mayakan Boko Haram Sun Kai Sabon Hari a Yobe, Sun Tafka Gagarumar Barna

Mayakan Boko Haram Sun Kai Sabon Hari a Yobe, Sun Tafka Gagarumar Barna

  • Mayaƙan Boko Haram sun kai sabon hari a ƙauyen Kukarera na ƙaramar hukumat Damaturu a jihar Yobe
  • Miyagun ƴan ta'addan sun halaka wasu ma'aikatan gine-gine mutum biyu tare da yin awon gaba da wasu mafarauta uku
  • Ƴan ta'addan sun kuma ƙona gida da motar Hakimin ƙauyen tare da lalata wani gida ɗaya a yayin harin da suka kai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Wasu ƴan bindiga da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kashe wasu ma’aikatan gini guda biyu tare da yin garkuwa da wasu mafarauta uku, a ƙauyen Kukareta da ke kan titin Maiduguri a ƙaramar hukumar Damaturu ta jihar Yobe.

Ƴan ta’addan sun kai hari garin ne a ranar Lahadi da misalin karfe 3:00 na dare, inda suka yi harbe-harbe na kusan sa’a ɗaya kafin su yi garkuwa da wasu mutum uku da suka zo garin domin farautar fara, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da 'mata 55' ƴan rakon amarya ɗaki a jihar Arewa

Mayakan Boko Haram sun halaka mutum biyu a Yobe
Mayakan Boko Haram sun halaka mutum biyu a wani sabon hari a Yobe Hoto: Mai Mala Buni
Asali: Twitter

Hakimin garin, Alhaji Lawan Babagana ya shaida wa jaridar ta wayar tarho cewa, ƴan ta’addan sun ƙona gidansa da motarsa ƙirar Peugeot 504.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da mutum uku da ya ba masauki a gidansa.

Yadda lamarin ya auku

A kalamansa:

"Sun afkawa garin ne da misalin ƙarfe 3:00 na daren Lahadi suna harbe-harbe, sun banka wa gidana wuta, suka ƙona motata ƙirar Peugeot 504, sannan suka lalata gida ɗaya a garin.
"Akwai mutum biyar a gidana da na ba masauki, biyu daga cikinsu ma’aikatan gine-gine ne da hukumar raya yankin Arewa maso Gabas ta kawo daga Adamawa, domin gina kasuwar Kukareta.
"Kamar yadda ka sani, a matsayina na sarkin gargajiya, na kan karɓi baƙuncin mutanen da ke zuwa yankina. Waɗannan yara (mayaƙan Boko Haram) sun fito da waɗannan (ma'aikatan) daga gidana, suka harbe su nan take.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara kan ƴan ta'adda, sun sheƙe masu yawa

"Akwai masu farautar fara mutum uku, waɗanda na ba masauki a gidana. Su (ƴan ta’addan) sun ɗaure su, suka yi awon gaba da su a cikin motar ƴan banga, wacce ke a gidana.
"Jami’an ƴan sanda sun kwashe gawar ma’aikatan ginin tare da kai su asibitin kwararru da ke Damaturu.

Mayaƙan Boko Haram Sun Farmaki Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe

A wani labarin kuma, kun ji cewa mayaƙan Boko Haram sun kai hari kan cibiyar tattara sakamakon zaɓe Kukareta da ke jihar Yobe.

Ƴan ta'addan na Boko Haram a yayin harin a garin da yake kan titin Maiduguri zuwa Damaturu, sun halaka mutum biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng