Bayan Shafe Kusan Mako a Hannun ’Yan Bindiga, Dalibai da Malaman Makaranta Sun Shaki Iskar ’Yanci

Bayan Shafe Kusan Mako a Hannun ’Yan Bindiga, Dalibai da Malaman Makaranta Sun Shaki Iskar ’Yanci

  • An sako dalibai da malaman makarantar da aka sace a jihar Ekiti a makon da ya gabata, an hasko bayanai
  • An sace dalibai da malamansu da yammacin ranar Litinin din da ta gabata, lamarin da ya tada hanhkali
  • Najeriya na ci gaba da fuskanar satar jama’a daga tsagerun ‘yan bindiga, musamman a Arewacin kasar

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Jihar Ekiti - An sako yaran makarantar Apostolic Faith Group of Schools da ke Emure-Ekiti, jihar Ekiti da aka sace tare da malamansu a kwanan nan.

An gano cewa, wadanda lamarin ya shafa sun shaki iskar ‘yanci ne da da misalin karfe 2:00 na safiyar Lahadi.

Yaran da malamansu sun kasance a hannun tsagerun masu garkuwa mutane da kusan kwanaki bakwai kenan yanzu.

Kara karanta wannan

'Yan makarantar Ekiti: An bar yaranmu da yunwa sannan ga duka, Iyaye

An sako daliban da aka sace a Ekiti
An sako daliban da aka sace a Ekiti bayan shafe lokaci a hannun tsageru | Hoto: @ekitistategov, ChuksEricE
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta yaya aka gano sun kubuta?

A cikin wani gajeren faifan bidiyo da ya yadu, an ga daliban da aka sako tare da malamansu zaune a kasa a gajiye, inda aka ji wata na koka halin da yaronta ke ciki.

Daily Trust ta ruwaito cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci Naira miliyan 100 domin a sako mutanen a baya, amma ba a tabbatar da ko an biya kudin fansa ko a’a ba ya zuwa yanzu.

Sai dai, daga baya sun rage kudin zuwa miliyan 15, wanda shi ma har yanzu ba a tabbatar ko an biya ba kafin sakin daliban, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ta yaya aka sace su tun farko?

An sace daliban da malamansu a cikin wata motar bas da ke dauke su a hanyar maida su gida bayan tashi a makanranta a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga da suka sace 'yan makarantar Ekiti sun yi barazanar kashe su

A nan ne suka gamu da tsagerun ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa dasu tare da bayyana neman kudin fansa.

Mutum nawa aka sace a harin?

Kimanin mutane 10 ne da ke cikin motar bas din – dalibai biyar, malamai uku da direba – aka yi garkuwa da su.

A ranar Asabar din da ta gabata ne dai aka yi ta yada jita-jitar cewa an saki mutanen, wanda ‘yan sanda suka musanta.

An sace mazakutar malamin allo bayab kasha shi

Wani mummunan yanayi ya auku, inda aka hallaka malamin makarantar allo kana aka yanke al'aurarsa.

Wannan lamari ya faru ne a Zaria a daidai lokacin da ake shirin auren wannan malamin da bai ji ba bai gani ba.

na zargin wasu tsagerun matsafa ne da aikata wannan aika-aika da ke kama da aikin tsafi da barnar ganganci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.