'Yan sanda sun kori wakilan Kwankwaso a wurin auren diyar Dangote

'Yan sanda sun kori wakilan Kwankwaso a wurin auren diyar Dangote

Rahotanni daga jihar Kano na nuni da cewar jami'an tsaro sun kori wakilan tsohon gwamnan Kano kuma Sanatan Kano Ta Tsakiya wato Dr. Rabiu Musa Kwankwaso daga wajen daurin auren 'yar hamshakin dan kasuwa Fatima Aliko Dangote.

Majiyar ta tabbatar da cewa bayan shigar su wajen aka rika fito da su daya bayan ana umartar su da su bar wurin daurin auren.

'Yan sanda sun kori wakilan Kwankwaso a wurin auren diyar Dangote
'Yan sanda sun kori wakilan Kwankwaso a wurin auren diyar Dangote

Babu wani takamaiman dalilin da jami'an 'yan sandan su ka bayar na korar wakilan na Kwankwaso.

KU KARANTA: Mutane da dama sun mutu sakamakon barkewar rikici tsakanin Hausawa da Yarbawa a Legas

Wasu ma su fashin baki a kan al'amuran dake faruwa a jihar Kano, musamman tsakanin tsohon gwamna Kwankwaso da gwamna mai ci, Ganduje, na alakanta korar wakilan Kwankwaso da kalamansa a kan daurin auren diyar gwamna Ganduje da dan gwamna Ajimobi.

Kwankwaso ya soki auren diyar Ganduje da cewar auren zawarawa ne, kalaman da ba su yiwa bangaren magoya bayan gwamna Ganduje.

Ma su nazarin siyasar Kano na ganin cewar abu ne mai matukar wuya a iya yin sulhu tsakanin tsohon gwamna Kwankwaso da gwamna Ganduje, tsohon mataimaki ga Kwankwaso.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164