Babban Nasara: Sojoji Sun Sheke ‘Yan Ta’adda 185, Sun Kama Wasu 212
- Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun yi gagarumin nasara a ayyuka daban-daban da suka gudanar a fadin kasar
- Hedkwatar tsaro ta bayyana cewa a cikin makon da ya gabata, sojoji sun sheke 'yan ta'adda 185 tare da kama wasu 212
- Haka kuma, sun kama barayin mai da ceto mutane 71 da aka yi garkuywa da su, tare da kwato makamai iri-iri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Hedkwatar tsaro ta ce dakarun sojoji dake aiki fadin kasar sun yi nasarar hallaka 'yan ta'adda 185 tare da kama wasu 212 cikin makon da ya gabata.
An tattaro cewa dakarun sojin sun kuma kama barayin mai 44 tare da ceto mutum 71 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su.
Daraktan labarai na ayyukan tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, 2 ga watan Fabrairu, jaridar The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu abubuwa sojojin suka yi nasarar kwatowa?
Ya ce dakarun sojin sun kwato lita 815,980 na danyen mai da aka sace, da lita 163,675 na man dizal da aka tace ba bisa ka’ida ba, da kuma lita 1,750 na kananzir.
A cewar kakakin rundunar tsaron, dakarun soji a yankin Niger Delta sun kuma gano tare da lalata rijiyar mai 12, jiragen ruwa 61, tankokin ajiyar mai 56 da ababen hawa 13.
Sauran kayayyakin da aka kwato sun hada da tukwanen gas 78, famfon zuba mai hudu, da wuraren tace mai da basa bisa ka'ida guda 56, rahoton Leadership.
Bugu da kari, sojojin sun kwato makamai iri-iri guda 224 da alburusai 2,337, da suka hada da bindigogi kirar AK47 guda 113, bindigar G3 daya, bindigar PKT daya, bindigu na gida guda 44 da sauransu.
'Yan bindiga sun sace 'yan sanda 3
A wani labarin, mun ji cewa wasu 'yan bindiga da ake zaton makiyaya ne sun yi garkuwa da jami'an yan sanda uku da ke aiki a PMF 51, Oghara, a garin Ohoror da ke karamar hukumar Ughelli ta arewa, jihar Delta.
Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, masu garkuwa da mutanen sun kuma yi awon gaba da bindigogin AK47 da harsasan yan sandan, sannan suka tisa keyarsu cikin daji.
Asali: Legit.ng