Fitaccen Malamin Addini Ya Tona Asirin Masu Juya Tinubu, Ya Fadi Barazanar da Za Su Fuskanta
- Fasto Olabisi Adegboye ya bayyana manyan mutanen da ke juya gwamnatin Shugaba Tinubu da ke kawo cikas
- Fasto Olabisi ya ce ana shan wahala a wannan gwamnatin ne saboda wasu masu son ransu sun yi kaka-gida a gwamnatin
- Amma Olabisi ya ce ubangiji ba zai barsu ba idan har ba su yi biyayya ba ga kudurorin Tinubu za su bar wurin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Babban Faston cocin Worksword of God, Olabisi Adegboye ya bayyana masu juya akalar gwamnatin Tinubu.
Olabisi ya ce ana shan wahala a wannan gwamnatin ne saboda wasu masu son ransu sun yi kaka-gida a gwamnatin.
Mene Faston ke cewa kan Tinubu?
Adegboye ya ce ubangiji ya zabi Shugaba Tinubu ne don ya masa aiki amma wasu ba su son ganin shugaban ya cimma burin hakan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce wadannan mutanen za a kore su kafin ya cika shekara daya idan har ba su yi biyayya ga kudurorin shugaban ba, cewar Tribune.
Ya kara da cewa mutanen sun hana Tinubu sanin me ake ciki kuma da neman yadda zai hadu da wasu don gyara kasar.
Barazanar da suke fuskanta
Ya ce:
“Wasu na jikin Shugaba Tinubu ba su son malaman addini su hadu da shugaban duk da sadaukar da kansu da suka yi don goyon bayansa.
“Tinubu ya na kan mulki ne don yin aikin ubangiji amma wasu masu son rai sun mamaye shi don biyan bukatar kansu.
“Ubangiji ba ruwansa da kowa, idan ba a yi sa’a ba Tinubu zai kasance a ofis su kuma za a sauya su, kowa za a iya sauya shi.”
Ya ce Ubangiji ba zai bari su ci gaba da abin da suke yi ba zuwa tsakiyar wannan shekara idan har ba su dawo kan hanya ba.
Minista ya fadi amfanin cire tallafi
Kun ji cewa Ministan yada labarai, Muhammad Idris ya bayyana amfanin cire tallafin mai a Najeriya.
Idris ya ce tabbas cire tallafin ya taimaki kasar wurin yin amfani da kudaden don yin ayyukan ci gaban kasar baki daya.
Asali: Legit.ng