Abuja: ‘Yan Bindiga Sun Nemi Karin Babura 2 Bayan Sun Karbi Kudin Fansa Naira Miliyan 8.5
- 'Yan bindigan da suka yi garkuwa da mutane a yankin Bwari dake babban birnin tarayya Abuja sun nemi a kawo masu babura biyu
- Hakan ya biyo bayan naira miliyan 8.5 da suka karba a matsayin kudin fansar mutanen amma sai suka ki sako su
- An rahoto cewa maharan sun yi barazanar kashe mutanen idan har aka yi jinjiri wajen kawo kudin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Abuja - 'Yan bindigan da suka karbi naira miliyan 8.5 kafin sako mutane hudu cikin 17 da suka sace, a Kawu dake yankin Bwari na babban birnin tarayya, sun bukaci sake bas sabbin babura kirar Bajaj biyu kafin su sako sauran mutum 11.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan bindigan sun yi garkuwa da mutanen 23 ciki harda wata mai jego a garin Kawu a ranar 26 ga watan Janairun 2023.
Hudu daga cikin mutanen sun tsere, inda suka bar 17 a hannun masu garkuwa da mutanen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani barazana 'yan bindigan ke yi?
An rahoto cewa 'yan bindigan sun yi barazanar kashe sauran mutanen 11 idan har aka yi jinkiri wajen biyan kudin fansar.
Da yake zantawa da jaridar Daily Trust a ranar Juma'a, wani dan uwan daya daga cikin mutanen da aka sace, Bala Dantani, ya ce an biya kudin fansar ne a rukuni-rukuni.
Ya ce an hada kimanin naira miliyan 5 sannan aka mika kudin ga 'yan bindigan, bayan sun yi barazanar kashe wadanda aka sacen makonni biyu da suka wuce.
A cewarsa, an kai wa 'yan bindigan naira miliyan 3.8 a ranar Talata, tare da kayan abinci da magunguna da kuma lemuka, bayan shugaban nasu ya yi alkawarin sakinsu, rahoton LIB.
Ya ce:
"Kuma yayin da muke jiran kiransu don jin inda za mu dauki mutanen a wannan rana ta Talata, mutumin da ya kai masu kudin fansa ya sake dawowa cewa 'yan bindigar sun kuma bukaci a kawo masu babura biyu kafin su sauko sauran mutanen 11."
Harin 'yan bindiga: Gwamnonin PDP sun ziyarci Filato
A wani labarin, mun ji cewa kungiyar gwamnonin PDP ta bayar da gudunmawar naira miliyan 100 don tallafawa wadanda hare-haren 'yan bindiga ya ritsa da su a jihar Filato.
Miyagun 'yan bindiga sun kai hare-hare jihar wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka masu yawan gaske da miliyoyin naira.
Asali: Legit.ng