Labari Mai Dadi: Gwamnan Arewa Ya Sanar da Wani Muhimmin Aiki da Zai Yi Nan da 2027

Labari Mai Dadi: Gwamnan Arewa Ya Sanar da Wani Muhimmin Aiki da Zai Yi Nan da 2027

  • Gwamna Muhammadu Umar Bago na Neja ya bayyana babban tanadin da gwamnatinsa ke yi wa bangaren ilimi a jihar
  • Bago ya ce babban abun da gwamnatinsa ta sanya a gaba a kokarinta na yi wa bangaren ilimi gyaran fuska shine samar da jami'o'i 10 mallakinta
  • Gwamnan da ya ce suna son cimma wannan zuwa 2027 ya ce hakan zai kuma samar da ayyukan yi ga al'umma

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Niger - Gwamnan Neja, Umar Bago, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta kafa jami'o'i 10 mallaki jihar zuwa shekarar 2027.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin kungiyar ci gaba ta Think Lab, ya kuma ce hakan zai kara tabbatar da samuwar aikin yi.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun ba mutanen da hare-haren Filato ya ritsa da su gudunmawar miliyan 100

Gwamna Bago na shirin samar da jami'o'i 10 a jihar Neja
Labari Mai Dadi Yayin da Gwamna Ke Shirin Gina Jami’o’i Na Musamman Guda 10 a Jihar Arewa Hoto: Gov. Mohammed Umaru Bago
Asali: Facebook

Zan yi wa bangaren ilimi gyaran fuska - Gwamna Bago

Bago, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta jajirce don yi wa bangaren ilimi gyaran fuska a Neja tare da ba 'yan asalin jihar fifiko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce abun da ya sanya a gaba shine samar da jami'o'i mallakar gwamnati guda 10 a fannoni daban-daban nan da shekara ta 2027.

Bago ya ce:

"Ina da burin samun jami'o'i guda goma na jihar daga yanzu zuwa 2027..
"Jihar Neja na da jami'ar Abdulkadir Kure wanda ke kan gudana, Jami’ar Noma dake Mokwa, Jami’ar Fasaha ta Zungeru, da kuma wata Jami’ar Kimiyyar Lafiya a Suleja.
“Wadannan su ne sabbin jami’o’i hudu da za su fara aiki. Kuma wasu za su biyo baya nan ba da jimawa ba."

Kungiyar Think Lab ta bayar da tallafi ga dalibai a Neja

Kara karanta wannan

"Ina cikin damuwa" Gwamnan PDP ya faɗi halin da yake ciki saboda rikicin siyasar jiharsa

A wajen taron, Bago ya ce kungiyar Think Lab za ta dauki nauyin jarrabawar UTME da SSCE na dalibai 10,000 daga makarantun sakandare na gwamnati a jihar Neja na 2024.

Ya bayyana cewa kungiyar ci gaban za kuma ta bayar da tallafin karatu kyauta ga dalibai 1530 domin su samu damar tafiya jami'a.

Bago ya kuma bukaci karin kamfanoni da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na zamantakewa don samar da ci gaba a fannin ilimi.

Said Kori, shugaban kungiyar Think Lab, ya ce kungiyarsa ta himmatu wajen samar da ci gaba mai dorewa tare da ajandar gwamnan na 2027.

Ya ce kungiyar ta gano dalibai biyar mafi hazaka wanda ke a ajin karshe daga makarantun sakandaren gwamnati 306 na jihar Neja kuma za ta ba su fifiko.

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin wasu mazauna Neja kan wannan yunkuri da gwamnan jihar ke yi.

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamna a APC ya yi alkawarin yin wa'adi 1 kacal a kan mulkin jihar, ya fadi dalilansa

Malam Abubakar ya ce:

“Mu dai babu abun da za mu ce kan wannan gwamnati na Bago don muna gani a kasa. Gwamnan mu na aiki iya bakin kokarinsa. Duk wanda ya shigo garin Minna ya san an samu sabon sauyi.
“Muna kyautata masa zaton cewa zai iya kuma zai cimma wannan kudiri nasa, abu ne da ya saba cimma duk abubuwan da ya sanya a gaba.”

Malama Fatima kuwa cewa ta yi:

“Shakka babu idan har aka cimma wannan za a samu gagarumin sauyi a harkar ilimi, koda dai mun san hakan zai tabbata.
“Misali ai yanzu aiki ake yi tukuru na kammala asibitin koyarwa don fara karatun likitanci a jami’ar IBB da ke Lapai, kuma hakan ya kasance ne saboda jajircewar gwamnan.
“Muna yi masa fatan alkhairi, mu dai al’ummar Neja yanzu muka yi gwamna.”

Ba na adawa da hijabi - Bago

A wani labarin kuma, mun ji cewa Gwamna Umar Bago ya yi watsi da rade-radin cewa gwamnatinsa tana adawa da sanya hijabi da malamai mata ke yi a jihar.

Gwamnatin a wata sanarwa da ta fitar ta bayyana cewa ko kadan ba ta adawa da sanya Hijabi ba kuma za ta taɓa yi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng