Sojojin Kasa Sun Bindige Wasu Mutane a Wajen Koyon Harbe-Harbe a Bariki

Sojojin Kasa Sun Bindige Wasu Mutane a Wajen Koyon Harbe-Harbe a Bariki

  • A yunkurin harbe-harbe kamar yadda sojoji suka saba domin samun kwarewa, an harbi wasu mutane
  • Sojojin da ke aiki a barikin 1 Division a Odogbo da ke garin Ibadan sun harbe mutane biyu da tsautsayi
  • Wani mazaunin Odogbo yace tun dare suke fama da harbe-harbe a bariki, hakan ya jawo bacin rana

Oyo - Jama’a sun shiga tashin hankali a kusa da barikin sojojin kasa na 1 Division da ke Odogbo a garin Ibadan yayin da aka samu tsautsayi.

Rahoton da jaridar Punch ta fitar dazu ya bayyana cewa mutane biyu aka harba da harsashi a yayin da sojojin kasa suke koyon harbin bindiga.

Wata majiya ta shaida cewa harsashin sojojin ya kubuce ya samu wani karamin yaro da bai wuce shekara 10 ba, an bada sunansa da Daniel.

Kara karanta wannan

An Gwabza Yaki Tsakanin Boko Haram, ‘Yan ta’adda Sun Kashe Kansu da Kansu

Baya ga haka, sojojin sun samu wani babban mutumi da aka fi sani da Baba Ajeri a Odogbo. Legit.ng ta tabbatar da labarin nan yau da yamma.

An kai mutane 2 asibiti

An ruga da wadannan mutane biyu zuwa asibitin da ke cikin barikin sojojin kasan na Odogbo, kuma mun samu labari cewa kokarin duba su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsautsayi ya rutsa da Bayin Allahn ne a ranar Juma’ar nan, harsashin wasu sojojin da ke gwaji ya auka masu bayan ya shiga cikin gidajensu.

Sojoji
Motocin Sojojin Kasa Hoto: Daily Trust, dailytrust.com
Asali: Facebook

Kamar yadda mu ka samu rahoto, harsashin sojojin ya dagargaza rufin kwanoni, wannan ya sa mutane da-dama suka yi zamansu a gida.

Mutane sun shiga dar-dar

Alhaji Kareem Ijeru wanda shugaba ne a unguwar, ya shaidawa manema labarai cewa harbe-harben sojojin ya yi kamari tun daga daren yau.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da mazauna suka tsere, an hallaka dan banga, an sace mutane a Neja

Saboda tsoron hasashi ya kai masu, mutanen unguwar sun ajiye motocinsu a wajen gida. Ba wannan ne karon farko da aka yi wannan ba.

“Sun fara, haka muke fama da wannan na tsawon shekaru. Sun fara a jiya, abin ya yi kamari a daren yau.
“Kowa ya shige gida, duk mun kwanta a kasa domin gudun harsashi ya same mu a cikin gidajen na mu.
An cigaba da harbe-harben har yau da safe, abin takaicin, an harbi mutane biyu, an sheka da su asibitin bariki.
Ba a cire harsashin jikin Baba Ajeri ba, amma Daniel ya ci sa’a, an fada mani an cire harsashin da aka harba shi.
- Alhaji Kareem Ijeru

B/Haram na kashe junansu

Dazu ne muka ji labari cewa rigima ta barke a tsakanin ‘yan kungiyar ISWAP da wasu sojojin Abubakar Shekarau, an rasa sojoji takwas.

Ana tunanin wasu ‘Yan Boko Haram sun gamu da fadan da ya fi karfinsu ne a lokacin da suka je yin fashi da makami wajen dakarun ISWAP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel