Gyara kundin tsarin mulkin Najeriya bata lokaci da asarar dukiya ne kurum inji NEF
Kungiyar NEF ta manyan Arewa ta soki shirin da majalisar dattawan ta ke yi na sake yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 garambawul.
NEF ta ce wannan aiki da ‘yan majalisar su ke neman su yi bai da wani amfanin kirki, sai dai ma kungiyar ta na ganin cewa za a bata lokacin da aka saba ne.
Darektan yada labarai da wayar da kai na NEF, Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya yi wannan jawabi a wajen wani taro da manema labarai a birnin tarayya Abuja.
Da ya ke magana a ranar Lahadi, Hakeem Baba-Ahmed, ya shawarci ‘yan Najeriya da su ki yin na’am da wannan aiki a lokacin da tattalin arzikin kasa ke kuka.
Jaridar Daily Trust ta rahoto mai magana da yawun bakin NEF din ya na cewa tun 2011, majalisa ta kan ware Naira biliyan 1 da sunan za a gyara kundin tsarin mulki.
Baba-Ahmed ya yi kira ga majalisar dattawa ta maida hankali wajen kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo karshen kashe-kashen da ake yi a Arewa.
KU KARANTA: Shugaban kasa ya dauki matakin kawo karshen rikice-rikicen APC
NEF ta nemi majalisa ta yi watsi da wannan tunani ‘na barna’ da ta saba yi kamar wani abin kwarai. Duk shekaru hudu a kan bijiro da wannan aiki da ya ke cin kudi.
"Kusan kowace majalisa tun 1999 ta kan batar da makudin kudin ‘yan Najeriya wajen aikin shirmen da su ke ganin su na yin abin da mafi yawan al’ummar kasa su ke so ne."
Dr. Baba-Ahmed ya ce tun da ake yin wannan aiki na gyara kundin tsarin mulki, babu wani cigaba da aka gani ta bangaren siyasa da sha’anin tattalin arziki a Najeriya.
A dalilin wannan ne kungiyar dattawan Arewar ta yi kira ga Sanatoci su ajiye wannan aiki. Ya ce abin da ake bukata shi ne gyara sha’anin shugabanci, tsaro da harkar zabe.
Darektan kungiyar ya ce ba za a cin ma wadannan abubuwa da aka ambata ta hanyar kashe dukiya bini-bini ba. Sai dai kungiyar Afenifere ba ta tare da NEF a kan wannan.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng