Kano: Bayan Abba Kabir, Jigon NNPP a Jihar Ya Yi Magana Kan Hadewar Kwankwaso da Ganduje

Kano: Bayan Abba Kabir, Jigon NNPP a Jihar Ya Yi Magana Kan Hadewar Kwankwaso da Ganduje

  • Jamu Mohammed, jigon jam’iyyar NNPP a Kano ya yi magana kan hadakar da ake yadawa tsakanin APC da jam’iyyarsu
  • Jamu ya ce ba su da masaniya kan wannan shirin hadaka da ake ta yadawa don sasanta Sanata Kwankwaso da Umar Ganduje
  • Jigon jam’iyyar ya bayyana haka ne a hira da gidan talabijin na Trust a yau Laraba 31 ga watan Janairu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Jigon jam’iyyar NNPP a Kano, Mohammed Jamu ya yi magana kan yiwuwar hadewar Kwankwaso da Ganduje.

Jamu ya ce ba su da masaniya kan wannan shirin hadaka da ake ta yadawa don sasanta Sanata Kwankwaso da Umar Ganduje.

Kara karanta wannan

Rikicin siyasar Kano: Ganduje ya tura sako mai muhimmanci game da alakarsa da su Kwankwaso

Jigon NNPP a Kano ya magantu kan sasanta Ganduje da Kwankwaso
Jigon NNPP a jihar Kano ya musanta sasanta Ganduje da Kwankwaso. Hoto: Umar Ganduje, Rabiu Kwankwaso.
Asali: Facebook

Mene jigon NNPP ke cewa kan Ganduje da Kwankwaso?

Jigon jam’iyyar ya bayyana haka ne a hira da gidan talabijin na Trust a yau Laraba 31 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce jam’iyyarsu ta NNPP ta ji maganar sansanta bangarorin biyu ne kadai a kafafen sadarwa.

Ya ce:

“Dukkan wannan abu da ake fada kan sasantawar muma daga Kano musamman jam’iyyar NNPP kawai muna jin hakan ne a kafafen sadarwa.”

Bayan tambayarsa shin ko an tuntubi jam’iyyar NNPP kan lamarin, sai ya ce:

“Ba mu san da komai kan lamarin ba”.

Martanin Abba Kabir kan jita-jita

Wannan na zuwa ne bayan Tinubu ya bukaci shugaban jam’iyyar APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sasanta da Sanata Rabiu Kwankwaso.

Daga bisani Ganduje ya roki Gwamna Abba Kabir na jihar Kano da ya zo su hada kai don inganta siyasar jihar.

Kara karanta wannan

Yayin da ake kiran Kwankwaso zuwa APC, NNPP ta yi magana kan hadaka da sauran jam'iyyu

Har ila yau, an yi ta yada jita-jita cewa akwai wata yarjejeniya da aka kulla tsakanin gwamnan Kano da APC kan shari’ar Kotun Koli.

Ana zargin an bar wa gwamnan kujerarsa ne bayan ya amince da sharudan da aka gindaya masa da suka hada da komawa jam’iyyar APC.

Sai dai gwamnan ya musanta yin wata yarjejeniya da Tinubu ko APC kafin hukuncin Kotun Koli inda ya ce babu wannar maganar.

Abba ya musanta yarjejeniya da APC

Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir ya musanta kulla wata yarjejeniya da APC ko Shugaba Tinubu kafin hukuncin Kotun Koli.

Gwamnan ya ce babu wata barazana da zai kawar da shi daga ayyukan alkairi da ya ke yi ga jama’ar jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.