Wike Ya Fitar da Naira Biliyan 30.9 Don Yin Wani Babban Aiki a Abuja
- Nyesom Wike ya ba da umurnin fitar da naira biliyan 30.9 don yin gyara da sake fasalin wasu makarantu a Abuja
- Wike zai kashe naira biliyan 13.3 don gyara makarantu 40, sai kuma naira biliyan 13.1 na sabunta makarantu 18
- Akwai kuma naira biliyan 4.5 da ministan babban birnin tarayyar ya ware don yin aikin wasu makarantu hudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya (FCT) Nyesom Wike ya amince a fitar da naira biliyan 30.9 don gyara makarantu a Abuja.
Sakataren ilimi na FCT, Dokta Danlami Hayyo ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai jiya a Abuja.
Kudin da za a kashe akan kowacce makaranta
Dokta Danlami Hayyo ya ce amincewa da fitar da kudaden ya nuna fifikon da ministan ya ba wa bangaren ilimi, Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hayyo ya ce, za a kashe naira biliyan 13.3 don gyara da farfado da makarantu 40, wadanda za a kammala aikin su nan da kwanaki 100.
Ya kara da cewa za kuma a kashe naira biliyan 13.1 don sabunta fasalin wasu makarantu gaba daya, wanda za a fara da makarantu 18.
Wadanne gyare-gyare za ayi a makarantun?
Sakataren ya ce an tsara sabunta komai na makarantun domin saka sabbin ababen more rayuwa da kayan aiki na zamani.
Abubuwan da za a gyara sun hada da bandaki, dakunan kwanan dalibai, cin abinci da samar da kujeru da ruwa.
Ya ce za a kuma gyara makarantu hudu a kashi na biyu na tsarin sabunta ginin makarantun gaba daya a kan kudi naira biliyan 4.5.
Jerin makarantun da za a yi wa kwaskwarima
- Kwalejin kimiyya da fasaha ta Gwamnati, Kwali
- Kwalejin kimiyya da fasaha ta Gwamnati, Maitama
- Kwalejin kimiyya da fasaha ta Gwamnati, Kuje
- Kwalejin kimiyya da fasaha ta Gwamnati, Wuse II
Ya ce dukkan ayyukan za a kammala su ne kafin watan Mayun 2024 kuma Shugaba Bola Tinubu zai kaddamar da su a bikin cika shekara guda a kan karagar mulki.
Hayyo ya yabawa ministan kan yadda ya magance matsalar da ta kunno kai tsakanin malaman firamare da sakatariyar kananan hukumomin yankin.
Binani Vs Fintiri: Kotun Koli ta yanke hukuncin zaben Adamawa
A wani labarin, Kotun Koli a ranar Laraba, ta yanke hukuncin karshe kan shari'ar zaben gwamnan jihar Adamawa.
Kotun ta ce Ahmadu Fintiri shi ne halastacce kuma zaɓaɓɓen gwamnan Adamawa ba wai A'isha Dahiru ba.
Asali: Legit.ng