Kiwon Lafiya: Guji aikata wadannan abubuwa 5 bayan cin abinci

Kiwon Lafiya: Guji aikata wadannan abubuwa 5 bayan cin abinci

Akwai abubuwa da mutane ke yawan yi bayan sun gama cin abinci kamar kishingida ko yin barci da sauran su. Da dama daga cikin abubuwan da aka saba yi bayan cin abinci na da dadin aikatawa amma ya zama dole a guje su don kare lafiya. Masana sun ce aikata hakan na da matukar hatsari kuma yana iya haifar da matsala ga lafiyar mutum.

A guji aikata wadannan abubuwan guda 5 da zarar an gama cin abinci:

1) Shan sigari: Sigari nada sinadarin ''nicotine'' wanda ya ke haifar da ciwon daji da hunhu. Wannan illa ta sigari tana zama ninki goma idan aka sha sigarin da zarar an gama cin abinci. Har wayau shan sigari bayan gama cin abinci yana hana narkewar abincin da wuri. Idan ya zama dole sai an sha sigarin to a bari sai bayan kamar sa'a 2 (2 hours) bayan gama cin abincin.

2) Cin 'yayan itatuwa: 'Yayan itatuwa na dauke da sinadarai da suke daukan tsawon lokaci kafin su narke su bi jikin dan adam. Shan su kafin a ci abinci zai bada damar amfana da sinadaran gina jiki da suke dauke da su. Shan su kuwa bayan gama cin abinci na jinkirta narkewan abinci yana kuma gadar da zafi a zuciya da kuma yawan gyatsa.

Kiwon Lafiya: Guji aikata wadannan abubuwa 5 bayan cin abinci
Kiwon Lafiya: Guji aikata wadannan abubuwa 5 bayan cin abinci

3) Barci: Mutane da dama na yawaita yin barci da zarar sun gama cin abinci wanda hakan na sa kumburin ciki kuma yana sa barci na babu gaira babu dalili a lokutan da basu kamata ba. Bincike ya nuna cewa masu yawan yin barci da zaran sun gama cin abinci sun fi saukin samun cutar bugun zuciya (stroke). Yana da kyau a dakata akalla sa'a 2 bayan cin abinci kafin a yi barci.

DUBA WANNAN: Magani 5 da tafarnuwa ke yi a jikin dan Adam

4) Wanka: Yin wanka da ruwan dumi bayan gama cin abinci yana tsinka jinin jiki wanda hakan na hana jini isa ga tumbin dan adam. Hakan yana kawo cikas ga narkewan abincin da aka gama ci.

5) Shan Shayi: Shayi na da muhimmanci amma shan sa bayan an gama cin abinci yana kawo karancin sinadarin ''Iron''. Hakan na iya sanya jiri da rashin kuzari da gajiya. Har wayau karancin ''iron'' na iya kawo cutar (anaemia).

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel