Majalisar Tarayya Na Tuhumar Hukumar Kwastam Kan Wani Dalili Daya Tak
- Kwamitin binciken kudi (PAC) na majalisar tarayya ya tuhumi hukumar kwastam kan gaza gabatar da bayanan kudinta na shekaru uku
- Kwamitin na zargin akwai wasu kudade da hukumar ba ta saka a asusun gwamnati ba, wanda ya sa taki gabatar da bayanan
- Sai dai shugaban kwastam na kasa, Basir Adeniyi ya ce duk wasu bayanan shige da ficen kudin hukumar na hannun bankin CBN
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Majalisar tarayya ta caccaki hukumar kwastam kan gaza gabatar da bayanan shige da ficen kudin hukumar na tsawon shekara uku ga akanta janar na kasa.
Kwamitin majalisar kan binciken kudi (PAC) ya yi sukar yayin da shugaban hukumar kwastam na kasa Basir Adewale Adeniyi ya bayyana gaban sa.
Kwamitin ya gayyaci shugaban kwastam din ne bayan da akanta janar na kasar ya nemi jin ba'asin dalilin hukumar na kin gabatar da bayan kudinta na 2016, 2017 fa 2018.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubuwan da ake zargin hukumar kwastam da su
Ana zargin cewa hukumar kwastam ba ta cika kudin da ta saka a asusun gwamnati a 2017 ba da 2016 kamar yadda ta nuna ta saka a bayanan banki, Vanguard ta ruwaito.
Ana kuma tuhumar hukumar da karya dokar saka kudaden haraji, da kuma gaza gabatar da bayanan kudin kamar yadda doka ta tanada.
Sai dai shugaban hukumar ya ce akwai shaidar duk wasu kudi da hukumar ke sakawa a asusun gwamnati da wanda ba na gwamnati ba.
Shugaban kwastam ya kare hukumar daga zargi
Ya ce tun bayan da gwamnati ta bullo da tsarin asusun TSA hukumar ta daina saka kudin haraji a asusun bankuna sai dai zuwa asusun CBN.
A cewarsa, tun a 2009 hukumar ta daina amfani da littafin ajiye bayanan kudi na Book 6A, don haka ana iya ganin bayanan kudin a rahoton CBN.
Freedom Online ta ruwaito cewa wasu takardu da ya gabatarwa kwamitin, ya nuna cewa hukumar ta gabatar da bayanan kudinta na shekaru uku ga akanta janar a shekarar 2021.
Adamawa: Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Fintiri
A wani labarin kuma, Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Ahmadu Fintiri na jam'iyyar PDP a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Adamawa.
Jam'iyyar APC da 'yar takararta a zaɓen jihar na 2023, Aisha Dahiru ne suka shigar da kara gaban kotun don kalubalantar nasarar Fintiri.
Asali: Legit.ng