Gwamnoni 36 da Tinubu Sun Shiga Uku Bayan Maka Su a Kotu Kan Babban Kuskure 1, Bayanai Sun Fito

Gwamnoni 36 da Tinubu Sun Shiga Uku Bayan Maka Su a Kotu Kan Babban Kuskure 1, Bayanai Sun Fito

  • Jihohi 36 da ke Najeriya da birnin Abuja za su fuskanci hukunci bayan an maka su a kotu kan kudaden UBEC
  • Babbar lauya, Funmi Falana ita ta maka jihohin da Abuja kan rashin neman kudaden hukumar don ba da ilimi kyauta
  • Ta zarge su da kin neman kudaden wurin biyan wasu kudade don ba da ilimi kyauta ga yara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Babbar lauya a Najeriya, Funmi Falana ta maka jihohi 36 da Abuja a kotu kan kudaden hukumar UBEC.

Falana ta shigar da karar ce Babbar Kotun Tarayya da ke Legas kan rashin amfani da biliyan 68 na hukumar samar da ilimi daga tushe.

Kara karanta wannan

An gama biyan bashin daloli, bankin CBN ya dauko hanyar farfado da kimar Naira

An maka Tinubu da gwamnonin jihohi 36 a kotu
Am maka gwamnonin jihohi 36 kan rashin amfani da kukdden UBEC. Hoto: NGF, Funmi Falana.
Asali: Facebook

Mene ake zargin gwamnonin?

Ta zarge su da kin neman kudaden wurin biyan wasu kudade don samun dama da ba da ilimi kyauta ga 'yan kasar wanda hukumar ke bayarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran da ke cikin shari'ar sun hada da Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi da Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman.

Funmi ta ce hakan ya sabawa dokar kasa sashi na 11 na dokar hukumar da kuma kasa baki daya ta shekarar 2004, cewar Channels TV.

Ta bukaci kotun ta binciko mene ya hana jihohin biyan kudaden da suka dace don samun damar amfani da kudaden.

Wace bukata lauyar ta nema?

Lauyar ta kuma nemi kotun tilasta musu biyan kudaden don samun damar yin amfani da naira biliyan 68 cikin kwanaki 30 da shigar da karar.

Tun a shekarar 2005, jihohi 36 da kuma Abuja sun gaza yin amfani da biliyan 68 din da aka ware don taimakawa bangaren ilimi.

Kara karanta wannan

Kamar Kano, Gwamnatin Kebbi ta fara yi wa zawarawa auren gata

Har ila yau, yawan yaran da ba su zuwa makaranta kullum karuwa suke a fadin kasar musamman a Arewacin Najeriya.

Hukumar UNICEF ta fitar da wani rahoto da ke nuna yawan yaran ya kai miliyan 20 a kasar, Premium Times ta tattaro.

Wannan bai rasa nasaba da rashin amfani da kudaden don bai wa yaran ilimi kyauta wanda zai rage yawan yara da ba su zuwa makaranta a Najeriya.

An sace yara dalibai a Ekiti

A wani labarin, yayin da rashin tsaro ke kara kamari a Najeriya, mahara sun sace yara dalibai.

Wannan na zuwa ne kwana daya bayan hallaka manyan sarakunan gargajiya 2 a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel