Jerin jihohi 8 da ba za su iya rayuwa ba tare da tallafi daga asusun Gwamnatin Tarayya ba

Jerin jihohi 8 da ba za su iya rayuwa ba tare da tallafi daga asusun Gwamnatin Tarayya ba

Gwamnatocin jihohi a Najeriya suna samun kudaden shiga don biyan bukatunsu na yau da kullun daga asusun tarayya da kuma kudaden shiga (IGR).

Yayin da wasu ke da wadatan da za su iya rayuwa ba tare da samun kaso daga tarayya ba, akwai wasu da ba za su iya yin hakan ba idan babu tallafi daga gwamnatin tarayya.

Kididdigan ASVI na Tattalin Arziki ya nuna wasu jihohin da ba za su iya yi ba tare da kudaden shiga daga tarayya ba.

Jerin jihohi 8 da ba za su iya rayuwa ba tare da tallafi daga asusun Gwamnatin Tarayya ba
Jerin jihohi 8 da ba za su iya rayuwa ba tare da tallafi daga asusun Gwamnatin Tarayya ba Hoto: Douye Diri, Mai Mala Buni, Samuel Ortom, Adamawa State
Asali: Facebook

A cewar jaridar The Cable, ASVI ta auna ma'aunin jihohin da ke amfani da kudaden shiga da ake tattarawa na kowace jiha bisa kaso na asusun tarayya na shekara.

Legit.ng ta tattaro cewa jihohin da ke da IGR kasa da kashi 10% na jimillar kudaden da suke karba daga gwamnatin tarayya sune ake dauka a matsayin wadanda ba za su iya tsayuwa da kafafunsu ba.

Kara karanta wannan

Daga Obasanjo zuwa Buhari: Jerin basussuka da aka karbo a karkashin Shugabannin Najeriya 4

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga jerin jihohin da aka lissafa a matsayin waɗanda ba za su iya rayuwa ba tare da kason tarayya ba, a cewar ASVI:

1. Bayelsa: 8.0%

2. Jigawa: 8.1%

3. Katsina: 8.8%

4. Adamawa: 9.1%

5. Yobe: 9.2%

6. Neja: 9.6%

7. Taraba: 9.8%

8. Benue: 9.8%

A cewar rahoton, jihar Bayelsa ta sami jimlar Naira biliyan 152.54 a matsayin rabon tarayya a shekarar 2020 amma ta samar da Naira biliyan 12.18 ne kacal a matsayin IGR, wanda ke wakiltar kashi 8.0% na jimillar kudaden da ta samu daga asusun tarayya.

Jihar Jigawa ta samu naira biliyan 107 a matsayin kaso daga asusun tarayya amma ta samar da IGR na naira biliyan 8.6 ne kawai (kashi 8.1).

Mahaifar Shugaba Muhammadu Buhari ta Jihar Katsina ta samu Naira biliyan 130 a matsayin kudin da gwamnatin tarayya ta ware mata amma ta samu IGR na biliyan 11.3 (kashi 8.8%).

Kara karanta wannan

Bikin tunawa da ranar 'yancin kai: FG ta yi gargaɗi mai ƙarfi ga 'yan Najeriya gabanin 1 ga Oktoba

Jihar Adamawa da ke da IGR na Naira biliyan 8.3 ta sami Naira biliyan 91 a matsayin kaso daga tarayya (kashi 9.1%).

Jihar Yobe da ke da IGR na Naira biliyan 7.7 ta karbi Naira biliyan 84 a matsayin kason tarayya (9.2%) yayin da Neja da IGR na Naira biliyan 10.5 ta samu Naira biliyan 109 a matsayin abin da gwamnatin tarayya ta ware mata (9.6%).

Jihar Taraba da ke da IGR na Naira biliyan 8.1 ta sami Naira biliyan 82 a matsayin kason tarayya (9.8%) yayin da jihar Benue da IGR na N10.46 biliyan ta sami N106 biliyan a matsayin kason tarayya (9.8%).

Gwamnatin Buhari ta kashe N8.9tr a gina abubuwan more rayuwa a shekarar 2020

A wani labarin, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo yace gwamnatin tarayya ta kashe Naira tiriliyan 8.9 wajen gina abubuwan more rayuwa a 2020.

Yemi Osinbajo ya bayyana haka wajen kaddamar da rukunin gidajen Dakkada luxury estate a Uyo, Akwa Ibom a ranar Juma’a, 24 ga watan Satumba, 2021.

Kara karanta wannan

NDLEA Ta Kama Dillalin Miyagun Kwayoyi Da Hodar Iblis Na Biliyan 2.3 A Abuja

Farfesa Osinbajo yake cewa ba a taba yin gwamnatin da ta kashe kudi sosai domin samar da abubuwan more rayuwa ba irin ta Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel