"Idan Ba Za Ka Iya Ba Ka Sauka": Atiku Ya Caccaki Tinubu Kan Abu 1 Tak

"Idan Ba Za Ka Iya Ba Ka Sauka": Atiku Ya Caccaki Tinubu Kan Abu 1 Tak

  • Atiku Abubakar ya koka kan yadda gwamnati mai ci ta Shugaba Tinubu ke tafiyar da harkokin tsaro
  • Atiku ya zargi Tinubu da zura ido a matsayinsa na Shugaba yana kallon yadda rashin tsaro ya zama ruwan dare
  • Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar satar mutane da kashe-kashe a wasu wurare daban-daban na ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da rashin yin abin da ya dace don shawo kan matsalar rashin tsaro.

A makonnin baya-bayan nan, an samu rahotannin sace-sacen mutane a sassan babban birnin ƙasar nan, Abuja, da wasu wurare daban-daban a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Na hannun daman Atiku ya sake sanya labule da Tinubu a Paris, bayanai sun fito

Atiku ya caccaki Tinubu
Atiku ya yi Tinubu wankin babban bargo kan matsalar rashin tsaro Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Ku tuna cewa Tinubu ya bar Abuja zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa a wata ziyarar ƙashin kansa, a ranar Laraba 24 ga watan Janairu kuma ana sa ran zai dawo ƙasar nan a makon farko na watan Fabrairun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane martani Atiku ya yi?

Da yake mayar da martani, Atiku ya yi Allah-wadai da ziyarar da Tinubu ya kai ƙasar Faransa, a daidai lokacin da ƙasar nan ke fama da matsalar rashin tsaro wacce ta zama ruwan dare, inda ta ke zama barazana ga zaman lafiyar jama’a.

A cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na X, a ranar Talata, 30 ga watan Janairu, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya buƙaci Tinubu da ya sauka idan ba zai iya magance matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya ba.

Atiku ya wallafa a shafinsa na X cewa:

Kara karanta wannan

Shettima ya bayyana gaskiya kan shirin gwamnatin Tinubu na mayar da manyan ofisoshi zuwa Legas

"Tinubu ya yi tafiyarsa yayin da Najeriya ke nutsewa cikin kogin matsalar rashin tsaro. Shugaban ƙasa yana can wai wajen wata ziyarar ƙashin kansa yayin da masu garkuwa da mutane suka kashe wata mata mai shayarwa da tsohuwa a Abuja saboda kasa biyan kuɗin fansa N60m da halaka wasu sarakuna biyu a Ekiti, da sauran munanan abubuwan da ke faruwa kan ƴan Najeriya.
"Idan ƙasar ta yi wa Emilokan girma, to ya kamata ya sauka kawai. Najeriya ba ta buƙatar wani shugaban ƙasa mai yawo. Ƙasar nan tana buƙatar samun shugabanci na 24/7 domin fuskantar matsalar tsaro da tattalin arziƙin da ya durƙushe. -AA"

Al'amuran rashin tsaro

Atiku ya bayyana haka ne bayan wasu ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe wasu sarakunan gargajiya biyu a ƙaramar hukumar Ikole ta jihar Ekiti tare da sace wasu ƴan makaranta.

Har ila yau, a ranar Asabar, 27 ga watan Janairu, ƴan bindiga sun kashe wata mata mai shayarwa (matar wani ɗan sanda) da surukarsa a jihar Neja, bayan sun yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya bayyana abu 1 da ya hana kawo karshen matsalar tsaro a jiharsa

A baya-bayan nan, wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun sace wata mata da ƴaƴanta uku a Kaduna.

Atiku Ya Yi Martani Kan Kisan Nabeeha

A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar ya yi martani kan kisan da ƴan bindiga suka yi wa Nabeeha Al-Kadriyar a birnin tarayya Abuja.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya nuna alhininsa a kan kisan wanda ya bayyana a matsayin abun baƙin ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng