Yadda Mata Hudu Suka Mutu a Wajen Hakar Ma’adanai a Wata Jihar Arewa

Yadda Mata Hudu Suka Mutu a Wajen Hakar Ma’adanai a Wata Jihar Arewa

  • Akalla mata hudu ne aka ruwaito sun mutu sakamakon kasa da ta rufta kansu a wani wajen da ake hakar ma'adanai a jihar Bauchi
  • Wani daga cikin wadanda abin ya rutsa da su, ya ce talauci ne ya tilasta daruruwan mutane a yankunan zuwa hakar ma'adanai
  • Ba wannan ne karon farko da ake samun zabtarewar kasa a wuraren hakar ma'adani a jihar Bauchi ba, an yi asarar rayuka da dama

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Bauchi - Wani abin tashin hankali ya faru a wani wurin da ake hakar ma'adanai a jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya, inda mata hudu suka mutu a bayan kasa ta ruftawa kan su.

Kara karanta wannan

Miyagun 'yan bindiga sun kai ƙazamin hari, sun halaka ƴan sanda da wasu bayin Allah a jihar APC

A cewar wani ganau, matan hudu ba su iya tserewa daga wurin a kan lokacin da kasar ta zabatare ba, wanda ya zama silar ajalinsu.

Rami ya rufta kan mata hudu da ke hakar ma'adanai a Bauchi, sun mutu nan take
Rami ya rufta kan mata hudu da ke hakar ma'adanai a Bauchi, sun mutu nan take. Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Twitter

Wannan mummunan lamari dai ba shi ne irinsa na farko ba, mata da kananan yara da su ne galibin ma'aikatan na rasa rayukansu a wurin hakar ma'adanai a jihar Bauchi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin da ya sa jama'a ke zuwa hakar ma'adanai

A shekarar 2023, wani wurin hakar ma'adanai a Bar Kudu, cikin karamar hukumar Bogoro, ya lashe rayukan mata uku tare da jikkata wasu, kamar yadda gidan talabijin na AIT ya ruwaito.

Mathias Mamaki da mahaifiyarsa, mutane biyu da suka tsira daga wannan iftila'in, tare da Musa wanda shi ma yana wurin hakar ma'adanan ne suka bayyana abin da ya faru.

Musa ya ce tsananin talauci ne babban dalilin da ya sa daruruwan jama’a suka dunguma zuwa wurin da ake hakar ma’adinan domin hako sinadarin 'monoxide' don samun abin rayuwa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kwamushe mutum 10 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Akwa Ibom

An roki hukumomi su samar da matakan kariya

Tribune Online ta ruwaito daya daga cikin mazajen wanda abin ya shafa, Iliya Gambar, ya ce sun yi bakin cikin faruwar wannan abin iftila'in.

Ga mutane da yawa, abin da yafuwa zai zama kamar izina game da hatsarorin da ke tattare da yin aiki a wurin hakar ma'adanai ba bisa ka’ida ba.

An shawarci hukumomi da su samar da matakan tsaro da za su hana sake faruwar irin hakan a nan gaba.

Zulum ya nada sabon Wazirin Borno

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya nada Mutawali Shettima Bukar matsayin sabon Wazirin Borno kamar yadda Shehun Borno ya bukata.

Zulum ya nemi sabon Wazirin da ya ba da tashi gudunmowar wajen raya al'adu da wanzar da zaman lafiya a jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.