Zulum Ya Nada Mutawali Shettima a Matsayin Wazirin Borno
- Babagana Zulum ya nada Mutawali Bukar matsayin sabon Wazirin Borno bayan da Shehun Borno ya gabatar masa da sunansa
- Kafin nada shi sabon Wazirin, Mutawali Shettima ya rike mukamai da dama da suka hada da mataimakin magatakardar jami'ar Borno
- A fannin ilimi kuwa, yana da shaidar karatun diploma a fannin shari'a, da digiri a fannin ilimin Islama, kuma ya kware a yaruka uku
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum ya amince da nadin Mutawali Shettima Bukar a matsayin sabon Wazirin Borno.
Wannan nadin na zuwa ne bayan da Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garba Al Amin El-Kanemi ya mika sunan Bukar ga gwamnan don amincewarsa.
Nasarorin da Shettima ya cimma kafin zama Wazirin Borno
Kafin nadin nasa, Blue Print ta ruwaito cewa Mutawali Shettima shi ne mataimakin magatakardar jami'ar Borno.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma yi aiki matsayin mamba a hukumar gudanarwar kamfanin sarrafa taki na Maiduguri, da hukumar da'awar Musulunci, da shirin bunkasa kananan yara.
Hakazalika ya rike sarautun gargajiya da suka hada da Mala Kaka na Borno, Hakimin Gwange da Shettima Kanuribe na Borno.
Dalilin da ya sa aka nada Shettima Wazirin Borno
Sabon Wazirin Borno na da shaidar karatu ta diploma a fannin shari'a da kuma digiri a ilimin Islama. Ya kware a yaren Kanuri, Turanci da Larabci.
Zulum ya bayyana cewa an nada Mutawali Shettima ne bayan nazari kan irin kwarewarsa da kuma ayyukan ci gaban al'umma da ya yi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnan ya taya shi murnar zama Wazirin Borno tare da kuma fatan zai ci gaba da ayyukan da za su daga martabar al'adun Borno da zaman lafiya.
Zulum ya dauki mataki kan ciyamomin da ke fashin zuwa aiki
A wani labarin kuma, Gwamna Babagana Zulum, ya samar da wani tsari na daukar bayanan ciyamomin da ke zuwa aiki da wadanda ba sa son zuwa wajen aiki.
Zulum ya ce zai yi amfani da na'ura wacce ciyamomin za su rinka sa hannu har sau hudu a rana don tabbatar da cewa suna wajen ayyukan su tun safiya har zuwa lokacin tashi aikin
Asali: Legit.ng