Kanuri: Al'ada, addini, aure, abinci da tsatson babbar kabilar
- Kabilar Kanuri tana daya daga cikin manyan kabilun da suka mamaye yankin arewa maso gabas na Najeriya
- Kabilar tana da dogon tarihi wanda tsatsonta dole ne a danganta shi da kasar Yemen amma yanzu suna Borno
- Tun farkon kabilar, mabiya addinin Musulunci ne har zuwa yanzu, abincinsu abun birgewa ne
Kabilar Kanuri sananniyar kabila ce a kasarnan. A yadda tarihi ya nuna, kanuri itace sananniyar kabila a jihar Borno ta samu asali ne daga Yemen.
Menene asalin mutanen Kanuri?
Kanurin zamanin nan sun samo asali ne daga yan Sayfawa daga masarautar Kanem.
Sakamakon yaki da fadace-fadacen Bulala, an kori mutanen Kanuri daga Kanem a karni na 14, bayan shekaru aru-aru ana yaki, mutanen Kanuri sun kafa masarautarsu a kudu maso yammacin tekun Chadi.
A halin yanzu, yawancin Kanuri na zama a Borno dake arewa maso gabas a Najeriya, inda suka fi yawa.
Anfi sanin masarautar su da Bornu. Suna zama a wasu bangarorin Nijar, Chadi da Kamaru.
Akwai mutane da dama da suke zama wuraren da Saifawa suka koma wadanda ba'a san asalin tarihinsu ba.
Yanzu haka, ana kiransu Sau.
Ya al'adar Kanuri take?
Tabbas mutanen Kanuri suna da matukar kima a arewacin Najeriya. Suna girmama al'adunsu kwarai.
An san matan Kanuri da iya nuna kulawa. Suna yin kitso mai ban sha'awa da kuma lalle mai burgewa.
Mazan Kanuri kuwa, suna da alfahari; hakan yasa suka bambanta d sauran mazan arewa.
Basayin bara, sunada neman nakansu.
Idan kuwa aka zo rawa, ba'a barsu a baya ba. Domin sun iya takun burgewa. Sutturarsu kuwa sai dai ace MashaAllah! Saboda suna amfani da kaloli masu kayatarwa.
Ya rayuwar addinin mutanen Kanuri yake?
Mutanen Kanuri sun musulunta tun karni na 11 lokacin da Kanem ta zama tsakiyar wurin koyar da addinin Musulunci. Kuma har yanzu basu yada makamansu ba.
Mabiya sunnar ma'aiki ne kwarai.
Menene yaren mutanen Kanuri?
Mutanen Kanuri suna yaren Kanuri. Yaren guda biyu ne.
Akwai Manga Kanuri da kuma Yerwa Kanuri wanda akafi sani da Bare-bari.
A shekarar 1987, kimanin mutane miliyan 4 suke yin yaren a Najeriya, Nijar, Chadi da Kamaru da kuma wasu sassa na Libiya ta gefen Sudan.
Kanuri ne yaren da yake da jibi da masarautar Kanem da Bornu wadda ta mamaye tekun Chadi na tsawon shekaru dubu.
KU KARANTA: Osinbajo ya bayyana lokacin bude iyakokin kasar nan
KU KARANTA: ICPC ta bankado inda aka yi da N2.67 biliyan ta ciyar da 'yan makaranta
Ya auren yaren Kanuri yake?
Neman aure a yaren Kanuri na da sauki, kuma yayi daidai da yadda addinin Musulunci ya tanadar akan soyayya da aure.
Ana bukatar waliyyi, wato mai bayar da aure, zai iya zama mahaifi ko marikin yarinyar.
Akwai sadaki da siga, wadda itace tambaya tsakanin masu bada wa da masu amsa tsakanin dangin amarya da na ango, sai kuma shaidunsu.
Mafi karancin sadaki shine 1/4 din dinari. Don haka idan dinari ya kama N10,000, sadaki zai kama N2,500, wanda hakan akwai rangwame.
Sannan Ango zai zo ma da amaryarsa da kyaututtuka, sannan zai zo ma da Mahaifiyarta, yan uwan mahaifiyarta mata da maza, da 'yan uwanta, kakanninta maza da mata kyautuka na musamman.
Sannan idan za'a kai amaryar dakin mijinta, abokan mijin zasu biya kudin wanke kai, da na wanke hannu da kafa da man ja da madara.
Yanada kyau a san cewa, wadannan kyautukan saboda nuna daraja da kima da kuma soyayyar angon ga amaryarsa ne.
Abincin Kanuri
Abincin mutanen Kanuri sune gero da miya ko shinkafa da kuma masara.
Mutanen Kanuri suna farauta saboda samun nama. Suna kiwon shanu saboda nama, sannan suna shukar ganyayyaki da 'ya'yan itace saboda more rayuwa.
Hakika, rayuwar mutanen Kanuri na yin wata rayuwa mai ban sha'awa da sauki.
A wani labari na daban, akwai rade-radin da ke yawo a kasar Zazzau cewa gwamnatin jihar tana hararo nada Yariman Zazzau, Munir Jafaru a matsayin sabon sarkin Zazzau, lamarin da yasa aka tsananta tsaro a gidansa da ke Zaria.
Karagar mulkin Zazzau ta zama abun nema tun bayan rasuwar sarkin Zazzau na 18, Alhaji Shehu Idris a ranar 20 ga watan Satumban 2020.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng