Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Bam Sun Ragargaza ‘Yan Ta’adda a Jejin Birnin Gwari

Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Bam Sun Ragargaza ‘Yan Ta’adda a Jejin Birnin Gwari

  • Sojojin Operation Whirl Punch sun nunawa ‘yan ta’adda shayi ruwa ne a wani hari da aka kai
  • Rundunar sojojin sama tayi amfani da makamai ta bindige wani gungun miyagu a Birnin Gwari
  • ‘Yan ta’addan da aka kashe ne ake zargi suna da hannu wajen mutuwar wasu dakarun tsaro

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Dakarun Operation Whirl Punch sun samu galaba a kan ‘yan ta’adda ake zargi sun tasa mutane a gaba a Arewacin Najeriya.

Sojojin saman Najeriya sun bada sanarwar kashe wasu ‘yan ta’adda, Punch tace abin ya faru a karamar hukumar Birnin Gwari a Kaduna.

Sojoji
Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Birnin Gwari Hoto: Nigerian Air Force HQ
Asali: Facebook

‘Yan ta’adda 30 da ke kan babura aka sheka barzahu da luguden bama-bamai a garin Birnin Gwari da ya yi suna sosai wajen ta’addanci.

Kara karanta wannan

CBN: Duk da ana ta surutu, ma’aikata 1500 da ke Abuja za su fara aiki a Legas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda

A wani jawabi da aka samu daga ofishin Air Vice Marshal Edward Gabkwet, an ji cewa sojojin sun samu labarin motsin ‘yan bindiga ne.

Air Vice Marshal Gabkwet wanda shi ne Darektan hulda da jama’a da yada labarai yace ‘yan ta’addan ake zargi da alhakin kashe sojoji.

Kwanakin baya aka yi kwantan bauna, aka hallaka wasu dakarun sojoji a Kwanan Mutuwa bayan jerin nasarorin da aka samu a baya.

Ramuwar gayyar sojojin sama

Wadannan ‘yan ta’adda da aka ga bayansu ne ke da hannu a wannan danyen aiki da kuma wasu miyagun hare-hare da aka kai a yankin.

An rahoto Gabkwet yana cewa suna kokarin kawo karshen matsalar garkuwa da mutane a Arewa maso yamma da Arewa maso tsakiya.

Jawabin yace Operation Whirl Punch sun mamayi ‘yan ta’addan a Kwiga-Kampamin Doka.

Kara karanta wannan

Rahoto: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mutane 17, 000 a Karkashin Buhari da Tinubu

‘Yan ta’addan suna kan babura 15 dauke da makamai aka buda masu wuta ta sama, aka yi sa’a kuma aka kashe da-dama daga cikinsu.

An ceto mutane a Katsina

Sojojin kasa kuma sun bada sanarwar ceto mutane 35 da aka yi garkuwa da su a Katsina, rahotonmu yace an tsare su ne a jejin Dumburu.

Kwanan nan ‘yan bindigan suka dauke mutane daga Tashar Nagulle da Nahuta a Batsari, dawowarsu ya jefa al'ummar yankin a farin ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng