Miyagun Ƴan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari, Sun Halaka Ƴan Sanda da Wasu Bayin Allah a jihar APC
- Yan sanda da wasu mutane sun rasa rayuwansu yayin da wasu ƴan bindiga suka kai hari mai muni a titin Owerri zuwa Orlu a jihar Imo
- Wasu majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa maharan sun kashe ƴan sanda biyu da ke bakin aiki tare da wasu mutum 2
- Rahoto ya nuna da zuwan maharan suka buɗe wuta kan mai uwa da wani, suka tarwatsa masu sana'ar POS a yankin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Imo - Wasu ‘yan bindiga a ranar Litinin sun kai hari a mahadar Ohii da ke kan titin Owerri zuwa Orlu a jihar Imo inda suka kashe mutane akalla hudu.
Wasu majiyoyi sun ce biyu daga cikin wadanda suka rasa rayukansu ‘yan sanda ne da ke kan bakin aiki a yankin lokacin da ‘yan bindigar suka kai farmakin.
Wata majiya daga yankin ta shaida wa The Nation cewa ‘yan bindigar sun kai harin a cikin wata mota kirar Corolla SUV, suka bude wuta daga zuwansu wurin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin haka ne suka kashe mutanen kana suka tarwatsa masu sana'ar POS da ke kasuwanci a yankin.
A cewar majiyar, ƴan sandan guda biyu suna bakin aiki ne a yankin kafin harin ƴan bindigan ya yi ajalinsu.
A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda wakilin jaridar ya gani, an ga gawarwakin waɗanda suka mutu kwance cikin jini.
Maharan sun yi wa masu POS fashi
Bayanai sun nuna cewa ‘yan bindigar sun yi wa wani mai sana'ar POS fashi a Amawire–Orji da ke kan titin Owerri zuwa Okigwe.
Haka nan kuma wani daga cikin maharan ya je mahadar Christiana da ke kan titin Egbu tare da yi wa masu POS da dama fashi.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Imo, Henry Okoye, bai amsa kiran wayar salula da sakon tes da aka tura masa ba lokacin da aka tuntube shi.
Bam ya yi ajalin manoma a jihar Borno
A wani rahoton kuma Wani bam da ake zargin ƴan ta'adda ne suka dasa shi ya halaka manoma bakwai tare da jikkata wasu a jihar Borno.
Zagazola Makama ya ce lamarin ya auku ne da safiyar ranar Litinin a titin Pulka/Firgi da ke ƙaramar hukumar Gwoza.
Asali: Legit.ng