Babu Haram a Yanzu, Malamin Musulunci Ya Ce 'Yan 'Yahoo' Baza Su Shiga Wuta ba, Ya Girgiza Intanet

Babu Haram a Yanzu, Malamin Musulunci Ya Ce 'Yan 'Yahoo' Baza Su Shiga Wuta ba, Ya Girgiza Intanet

  • Shehin Malamin addinin Musulunci, Sheikh Atayese Jaqmal ya ce 'yan 'Yahoo' ba za su shiga wuta ba
  • Jagmal wanda ya sha jawo cece-kuce a karatuttukansa ya ce babu haram a halin yanzu da ake ciki
  • Ya ce a yanzu ana cikin wani hali babu wanda ya isa ya yanke maka hukuncin shi ga wuta ko aljanna

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kwara - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Abdul Wasiu Atayese ya rikita intanet saboda maganarsa ga 'yan 'Yahoo'.

Malamin da aka fi sani da Jagmal ya ce babu wani matsala dangane da ayyukansu.

Malamin addinin Musulunci, Sheikh Jaqmal Atayese ya girgiza Intanet
Sheikh ya birkita Intanet da kalamansa kan 'yan 'Yahoo'. Hoto: Sheikh Atayese Jaqmal.
Asali: Facebook

Maganar Jaqmal da ta jawo cece-kuce

Jagmal ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook inda ya wallafa faifan bidiyo da cewa babu haramcin hakan.

Kara karanta wannan

Gwamnan arewa ya cire tsoro, ya faɗi abu 1 da ƴan Najeriya zasu yi su samu sauƙi da ci gaba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce mutane za su ci gaba da cin haram har lokacin mutuwa, idan har don haram ne mutum ba zai shiga aljanna ba, to babu mai shiga.

Ya ce:

"Za mu ci gaba da cin haram har lokacin mutuwa, idan har don haram ne mutum ba zai shiga aljanna ba, to babu mai shiga.
"Babu wani abin haram, ko da matasa da ke yin 'Yahoo' ba za su kasance a wuta ba.
"Wace wuta za su shiga? Ba zai shiga wuta ba, idan ka ce dan 'Yahoo' zai shiga wuta meyasa ba za ja shi cikinta ba tun da kai ka kirkiri wutar."

Maganar malamin kan wuta da aljanna

Malamin ya kara da cewa a yanzu ana cikin wani yanayi, babu wanda ya isa ya ce za ka shiga wuta ko aljanna.

Kara karanta wannan

"Ku tuba ko a sheke ku": Wike ya gargadi masu garkuwa da mutane da masu yi masu leken asiri

Ya kara da cewa:

"Yanzu komai ya lalace, ba wanda ya isa ya ce za ka shiga wuta ko aljanna.
"Allah ne zai sa kowa inda ya ke so, amma abin da na ke da tabbaci shi ne mu malamai ba za mu shiga wuta ba."

An yanke wa Fasto hukuncin daurin rai rai

Kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukunci kan wani Fasto da ake zargin ya na lalata da mambobin cocinsa musamman mata.

Kotun ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai bayan samun shaidu daga wadanda abin ya faru da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.