Daliba Adamawa Ta Dauki Ranta Saboda Saurayinta Ya Rabu da Ita
- Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa wata daliba ta dauki ranta da kanta a jihar Adamawa saboda saurayinta ya ce su rabu da juna
- An ruwaito cewa dalibar na karatu ne a kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya da ke Mubi, kuma ana zargin malamin jami'ar MAU ne saurayin
- Iyayen dalibar mai shekaru 24 ne suka shigar da karar lamarin ga 'yan sanda, kuma an yi zargin ta sha gubar bera ne da ya halaka ta
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Adamawa - Wata daliba mai suna Jamima Shetima Balami ta dauki ranta da kanta ta hanyar shan wani abu da ake kyautata zaton gubar bera ne a jihar Adamawa.
Balami, dalibar ND II ce a sashen koyon aikin jarida a kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya da ke Mubi a jihar Adamawa a lokacin rasuwarta.
Balami, wacce ta fito daga Garkida Gombi, ta rasu ne a gidanta da ke Vinikilang, wanda aka fi sani da Hayin Gada a karamar hukumar Girei ta jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan sanda sun fara binciken musabbabin mutuwar Jamima
Dalibar mai shekaru 24, an ce ta dauki ranta ne lokacin da saurayin nata, da ake zargin malami ne a Jami’ar Modibbo Adama (MAU) ya bukaci su kawo karshen soyayyar su.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar (PPRO), SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Leadership a ranar Litinin.
Ya bayyana cewa mahaifin marigayiyar ne ya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda.
Nguroje ya kara da cewa, duk da cewa rahotannin da aka ba 'yan sanda ya bambanta, amma dai rundunar ta yi alkawarin gano ainihin musabbabin mutuwar yarinyar.
Ku kare kanku daga 'yan bindiga - Gwamnan. Katsina
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Katsina, Mallam Umaru Dikko Radda, ya nemi al'ummar jiharsa da su tashi tsaye su kare kansu daga hare-haren'yan bindiga.
Gwamnan ya ce gwamnati za ta ba su goyon bayan da taimako don kare kansu daga yan bindiga da masu garkuwa da suka addabi garuruwan jihar.
Ko a shekarar 2021, sai da tsohon gwamnan jihar, Aminu Bello Masari ya taba yin makamancin wannan furucin na cewa jama'a su sayi makamai don kare kansu a jihar.
Asali: Legit.ng