Fusatacciyar budurwa ta sha guba bayan ta gano wanda ya dirka mata ciki na da mata da 'ya'ya

Fusatacciyar budurwa ta sha guba bayan ta gano wanda ya dirka mata ciki na da mata da 'ya'ya

- Oluchi Akabilo budurwa ce mai shekaru 20 wacce ake zargi da yunkurin kashe kanta bayan cin amanarta da saurayinta yayi

- Wacce abin ya faru da ita 'yar asalin Ngbuka-Obosi ta sha wani abu ne da ake zargin maganin kwari ne don ta dauka ranta sakamakon barinta da saurayinta yayi

- A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed ya ce anyi kokarin kamo saurayin amma ya gudu

Oluchi Akabilo budurwa ce mai shekaru 20 wacce ake zargi da yunkurin kashe kanta bayan cin amanarta da saurayinta yayi. Saurayin dai sunan shi Chinedu kuma yana zama ne a Awada dake Onitsha a jihar Anambra.

Wacce abin ya faru da ita 'yar asalin Ngbuka-Obosi ta sha wani abu ne da ake zargin maganin kwari ne don ta dauka ranta sakamakon barinta da saurayinta yayi.

Jaridar The Nation ta gano cewa saurayin ya bata N10,000 ne ta zubar da cikin da ya dirka mata.

Majiya daga 'yan uwanta sun tabbatar da cewa ta sha gubar ne saboda ya gano cewa saurayinta mijin wata ne.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed ya ce anyi kokarin kamo saurayin amma ya gudu.

Fusatacciyar budurwa ta sha guba bayan ta gano wanda ya dirka mata ciki na da mata da 'ya'ya

Fusatacciyar budurwa ta sha guba bayan ta gano wanda ya dirka mata ciki na da mata da 'ya'ya
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Manyan kasashen duniya guda goma da suka fi farin ciki da jin dadin rayuwa

Ya ce: "A ranar 19 ga watan Maris din 2020 ne wajen karfe 4 na yamma aka kawo rahoto ofishin 'yan sandan Awada cewa wata budurwa mai suna Oluchi Akabilo ta sha maganin kwari don daukar rayuwar kanta.

"Budurwar ta samu ciki ne da saurayinta mai suna Chinedu amma ba ta sani ba ashe yana da mata har da yara. Ta matukar fusata bayan da ta gano cewa yana da aure.

"Abin da ya kara fusatata shine yadda ya barta babu kula. Budurwar ta yanke shawarar kashe kanta ne don ta dau kudin da ya bata don ta zubar da cikin ta siya gubar.

"An gaggauta mika ta asibiti a Onitsha don samun kulawar masana kiwon lafiya."

Mohammed ya kara da cewa, ana ci gaba da bincike don tabbatar da sahihin lamarin da ya jawo yunkurin kisan kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel