Budurwa mai shekaru 17 ta hallaka kanta ta hanyar kwankwadar piya piya a Jigawa

Budurwa mai shekaru 17 ta hallaka kanta ta hanyar kwankwadar piya piya a Jigawa

Rundunar Yansandan jihar Jigawa ta sanar da mutuwar wata budurwa mai shekaru 17 ta hanyar kwankwadar kwalbar piya piya, kamar yadda Kaakakin rundunar Jinji Abdu ya tabbatar.

Legit.ng ta ruwaito lamarin ya faru ne a ranar Litinin 2 ga watan Afrilu a kauyen Gambara dake cikin karamar hukumar Birnin Kudu na jihar. Sai dai Kaakakin yace:

“Labarin da muka samu ya nuna cewar budurwar mai suna Gambo Jibrin dake kauyen Gambara an kai ta asibitin garin Birnin Kudu bayan ta sha piya piya.

KU KARANTA: Yansanda sun cafke yan sara suka 23 da suka kashe wani tare da kona gidaje a Kaduna

“Samun wannan rahoto keda wuya muka aika da jami’anmu zuwa asibitin don tabbatar da gaskiyar rahoton, ko da suka je, sun tarar da budurwar tuni ta rigamu gidan gaskiya.” Inji Shi.

Sai dai yace tuni an mika gawar Gambo ga iyayenta don yi mata jana’iza kamar yadda Musulunci ya tanadar, ya kara da cewa tuni sun fara gudanar da bincike don gan musabbabin mutuwar yarinyar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel