Jihar Jigawa: Uwargida ta zubawa kishiyar ta gubar kashe bera a binci

Jihar Jigawa: Uwargida ta zubawa kishiyar ta gubar kashe bera a binci

Hukumar ‘yan sanda a jihar Jigawa t ace ta kama wata matar aure mai shekaru 45 (ba a bayyana sunan taba), da ake zargi da kasha kishiyar ta, tanhayar zuba mata gubar kasha beraye a cikin abinci a kauyen Kangal dake karamar hukmar Taura.

Kakakin hukumar ‘yan sanda a jihar, SP Abdul Jinjiri, ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai(NAN) na kasa a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Jinjiri y ace lamarin ya faru ne ranar 4 ga watan Mayu yayin da uwargidan ta dafa abinci amma sai ta zuba gubar a cikin kason kishiyar ta, Zulfa’u Amadu.

Jihar Jigawa: Uwargida ta zubawa kishiyar ta gubar kashe bera a binci
Kwalbar guba

Ya kara da cewar l;amarin ya faru ne kwana shida kacal da auro amarya Zulfa,u a kauyen Kangal dake karkashin karamar hukumar Taura.

Kamar yadda rahoton mu ya nuna, a ranar 4 ga watan Mayu, wacce ake zargi, a matsayin tan a uwargida ga mijin su, Malam Amadu, ta zuba gubar kasha beraye a kason abincin amaryar.

DUBA WANNAN: Majalisa na shirin daukan wani mataki mai tsauri a kan babban sifeton 'yan sanda

“Bayan amaryar ta ci abincin ne sai ta fara murkususun ciwon ciki kafin daga bisani a garzaya da ita asibiti inda ta mutu tun kafin a karasa.

Uwargidan ta musanta zargin da ake yi mata tare da bayyana cewar sun ci abinci daga kwano daya ne da amaryar da tuni aka binne ta bisa tsarin addinin Islama.

An dauki abincin ya zuwa asibiti domin gudanar da gwaji a kan sa, yayin da hukumar ‘yan sanda t ace zata gurfanar da uwargidan a gaban kotu da zarar ta kamala bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng