Mene Ma Aka Yi, Gwamnan APC Ya Magantu Kan Rashin Adalcin 'Yan Najeriya Ga Tinubu, Ya Ba da Tabbaci

Mene Ma Aka Yi, Gwamnan APC Ya Magantu Kan Rashin Adalcin 'Yan Najeriya Ga Tinubu, Ya Ba da Tabbaci

  • Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya bayyana himmatuwar Shugaba Tinubu kan kawo dukkan matsalolin kasar
  • Gwamnan ya ce rashin adalci ne a watanni takwas kacal cikin shekaru hudu a yanke hukunci musamman a tsaro da tattalin arziki
  • Ya ce ya na da tabbacin kawo karshen matsalar da ke damun kasar a nan da watanni kadan inda ya ce 'yan kasar za su yi dariya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya ce bai kamata tun yanzu a yanke wa gwamnatin Tinubu hukunci ba.

Uzodinma ya ce rashin adalci ne a watanni takwas kacal cikin shekaru hudu a yanke hukunci musamman a bangaren tsaro da tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Rikicin siyasar Kano: Ganduje ya tura sako mai muhimmanci game da alakarsa da su Kwankwaso

Gwamnan APC ya roki 'yan Najeriya su kara hakuri a mulkin Tinubu
Gwamna Uzodinma ya ce bai kamata tun yanzu a yanke hukunci kan gwamnatin Tinubu ba. Hoto: Hope Uzodinma.
Asali: Twitter

Mene Uzodinma ke cewa kan mulkin Tinubu?

Shugaban gwamnonin APC ya ce ya na da tabbacin Shugaba Bola Tinubu zai tsame 'yan Najeriya daga halin da suke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hope ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a jiya Lahadi 28 ga watan Janairu.

Gwamnan ya ce nan da 'yan watanni kadan kowa zai ga sakamakon matakan da shugaban kasar ke dauka a fannoni da dama.

Ya ce duk 'yan Najeriya za su zo su yi godiya daga baya saboda irin abubuwan da za su mora nan da watanni kadan, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Tabbacin da Uzodinma ya bayar kan mulkin Tinubu

Ya ce:

"Ni ne shugaban gwamnonin Kudu maso Gabas guda biyar kuma shugaban gwamnonin APC 20, dukkanmu kuma muna goyon bayan Shugaba Tinubu.

Kara karanta wannan

Rundunar Soji ta tona asirin mutum 2 da ƙarin wasu abubuwa da suka jawo kashe-kashe a Filato

"Kuma ina fada maka watanni bakwai ko takwas sun yi kadan ka yanke hukunci, mutane ba sa iya fahimtar abubuwa yadda suke gaskiya.
"Na amince idan har ka ga wannan mutumin bai kawo sauyi ba a wannan yanayi, to akwai matsala a wani wuri."

Tinubu ya kaddamar da kwamitin kara albashi

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya shirya yin magana kan batun mafi karancin albashin ma'aikata a Najeriya.

Shugaban ya kafa kwamiti don tattauna maganar mafi karancin albashi yayin da 'yan kasar ke cikin mawuyacin hali bayan cire tallafin mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.